Da yan uwana musulmai da kiristoci duk daya ne, gwamna Muhammed

Da yan uwana musulmai da kiristoci duk daya ne, gwamna Muhammed

  • Gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi yace gwamnatinsa ta ɗauki kiristoci da muhimmanci kamar yadda take wa musulmai
  • Muhammed yace yana gina manya-manyan coci-coci da masallatai domin nuna dai-daito tsakanin manyan addinan biyu
  • Yace gwamnatinsa ta kara yawan kiristoci a cikin harkokin gudanarwa fiye da gwamnatin baya

Bauchi - Gwamnan jihar Bauchi, Bala Muhammed, ya bayyana cewa kiristoci suna da yanci kwatankwacin na yan uwansu musulmai, wanda ya kamata a girmama.

The Nation ta rahoton Muhammed na faɗin haka yayin da shugaban kungiyar kiristoci, (CAN), Rabaran Abraham Damina, ya jagoranci tawagar kiristoci suka kai masa ziyara a Bauchi ranar Asabar.

Gwamnan yace a baya an watsar da kiristoci a harkokin gwamnatin jiha, amma gwamnatinsa ta kara yawan su a cikin gwamnatinsa domin nuna musu ana tare.

Bala Muhammed
Da yan uwana musulmai da kiristoci duk daya ne, gwamna Muhammed Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Haka nan kuma ya nuna gamsuwarsa da rawar da kiristoci ke taka wa a gwamnatinsa.

Kara karanta wannan

Za mu kama duk yaron da muka gani yana gararamba a titi a lokacin makaranta, Yahaya Bello

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Guardian ta rahoto gwamnan yace:

"Daga zuwan mu, mun fahimci an jingine kiristoci gefe ɗaya amma muka jawo su a jiki, muka kara yawan kiristoci a gwamnatin mu."
"Na yi farin ciki cewa a lokacin mu ne muka kara jawo kowa a jiki kuma muka kara samar da soyayya tsakanin mu. Sannan muka karya duk wani kokarin rarraba mu, wanda ya hana mu kallon juna a matsayin ɗaya."
"Muna gina manyan coci-coci kamar yadda muke gina masallatai saboda mun gano cewa dukka muna da yanci iri ɗaya kuma wajibi mu kiyaye muku yancin ku."

Zamu magance cutar da ake wa ma'aikata - Muhammed

Gwamna Muhammed ya ƙara da cewa gwamnatinsa za ta tabbatar da cewa zaluncin da ake wa ma'aikata ta hanyar zare su daga tsarin biyan albashi da gangan ya zama tarihi a Bauchi.

Kara karanta wannan

Babbar magana: Kwamishiniya a Zamfara ta yi murabus domin ta samu mukami a jihar Imo

Haka nan kuma yace gwamnatin jiha zata baiwa kananan hukumomi cikakken yanci, inda yace tuni aka fara tura musu kuɗaɗen su kuma sun fara biyan albashi da kansu.

A wani labarin kuma Kwamishinan Kogi yace ya ga ikon Allah kiri-kiri lokacin da yan bindiga suka farmake shi

Kwamishina ya bayyana irin halin da ya shiga yayin da yan bindiga suka farmake shi da niyyar yin awon gaba da shi.

Kwamishinan muhalli a jihar Kogi, Chief Victor Adewale Omofaiye, yace iko da mu'ujizar Allah ne ya tserad da shi daga sharrin maharan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262