Babu ruwana da rikicinku na APC a Kano, Shugaba Buhari ya yi fashin baki
- A wani sakon kar ta kwana, fadar shugaban kasa tayi watsi da jawabin wani jigon jam'iyyar APC a Kano
- Fadar shugaban kasa ta ce babu ruwan Buhari da rikicin APC Kano tun da lamarin na gaban kuliya
- Hakazalika an yi watsi da maganar da Shugaba Buhari ya nuna goyon bayansa ga wani tsagi
Abuja - Fadar Shugaban kasa ta yi fashin baki game da ikirarin da wasu yan siyasa a jihar Kano ke yi na cewa Shugaba Muhammadu Buhari na marawa wani tsagin baya.
Mai magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu, ya barranta maigidansa daga maganar marawa wani tsagi baya.
Ya bayyana hakan a jawabin kar ta kwana da ya saki da daren Asabar, 25 ga Disamba, 2021.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Za ku tuna cewa jam'iyyar All Progressives Congress APC ta rabe biyu a jihar Kano ana gab da gudanar zaben shugabannin jam'yyyar na jihar.
Yayinda Gwamnan jihar, Abdullahi Ganduje, ke goyon bayan tsagi guda, Tsohon Gwamnan jihar, Malam Ibrahim Shekarau ke jagorantar dayan tsagin.
Malam Garba Shehu yace:
"Fadar Shugaban kasa na watsi da jawabin da wani sagin APC a Kano ya saki cewa Shugaba Muhammadu Buhari na goyon bayansu."
"Wannan karya ne. Hakan ba zai yiwu ba kasancewar ana zama a kotu. Shugaba Buhari bai marawa kowa baya ba."
Kotu ta tabbatar da tsagin Shekarau matsayin sahihan shugabannin APC a Kano
Wata babbar kotun tarayya dake zamanta a birnin tarayya Abuja karkashin jagorancin Mai Sharia Hamza Muazu ta tabbatar da tsagin Shekarau ta gudanar da zaben shugabannin jam'iyyar APC a Kano.
Yayin Shari'a ranar Juma'a, Alkalin ya yi watsi da karar tsagin Ganduje kuma ya ci su tarar milyan daya kan batawa kotu lokaci, rahoton DailyNigerian.
Kotu ta tabbatar da cewa zaben da tsagin Shekarau tayi shine daidai kuma shugabanninsu ne shugabannin APC a jihar.
Abdullahi Abbas ne ke jagorantar tsagin Ganduje yayin da Ahmadu Haruna Zago ke jagorantar tsagin Shekarau.
Asali: Legit.ng