2021: Manyan farmaki 5 da 'yan bindiga suka kai wa hukumomin tsaro a fadin kasar nan
- Daga kudu har arewa, jami’an tsaro basu tsira ba daga hare-haren da ‘yan ta’adda su ka dinga kaiwa wanda ya yi sanadin rasuwar mutane da asarar dukiyoyi a shekarar 2021
- Yayin da kai hare-hare sansanonin jami’an tsaro a Najeriya ya zama ruwan dare, a shekarar 2021 lamarin ya kara kazanta inda masu ruwa da tsaki su ka dinga taro iri-iri
- Bincike ya nuna cewa an kai wa jami’an tsaro da sansanayensu farmaki a akalla fadin jihohi 30 da birnin tarayya, Abuja har wuraren da ba a taba tunani ba
Najeriya - Daga kudu har arewa, sansanonin jami’an tsaro sun fuskanci hare-hare iri-iri wadanda suka janyo rashe-rashen rayuka da dukiyoyi a shekarar 2021 a kasar nan.
Yayin da yanzu kai hari sansanonin jami’an tsaro ya zama ruwan dare, a shekarar 2021 lamarin ya kara kazanta wanda ya janyo masu ruwa da tsaki suka dinga yin taro iri-iri don shawo kan matsalar.
Binciken TheCable ya nuna cewa kusan jihohi 30 har da birnin tarayya wato Abuja sun fuskanci kalubalen tsaron wanda har ofisoshin jami’an tsaro ba a bari ba.
In banda a shekarar 2021, ba a taba kai farmaki makarantar horar da hafsoshin sojoji ta NDA ba, an kuma kai farmaki gidajen gyaran hali da ke Kogi, Filato, Oyo har da Imo sannan har banka wa ofisoshin ‘yan sanda wuta jama’a aka dinga yi.
Rahotanni sun bayyana wasu daga cikin hare-haren kamar haka:
Farmakin NDA
A karo na farko tun da aka kafa NDA wacce ke a Kaduna, ba a taba kai hari ba sai a ranar 21 ga watan Augusta inda wasu ‘yan bindiga suka yi dirar mikiya.
Lamarin ya shammaci jama’a don wuri ne na horar da jama’a a Najeriya, sai abin ya yi kama da hadin guiwa.
“Sun lallabo ne, duk da muna da wayoyin nan don haka ba ta katanga suka shiga ba. Sai dai a ranar babu sojoji don haka suka yi amfani da wannan damar inda suka samu sojoji uku,” kamar yadda wata majiya ta shaida wa The Cable.
Harin ya zama abin kunya a idon sojojin saboda har cikin wurin horon su aka bi su.
A lokacin aka yi garkuwa da wani manjo a NDA, Christopher Datong. Daga baya rundunar soji ta samu nasarar ceto shi bayan ya kwashe wata a hannun ‘yan bindigan.
Wannan harin ya janyo cece-kuce ta ko ina inda mutane suka dinga sukar gwamnatin tarayya.
Yadda fiye da ‘yan gidan yari 1,500 su ka tsere daga kurkukun Imo
A ranar 5 ga watan Afirilu wasu ‘yan bindiga suka kai farmaki gidan yarin Imo da hedkwatar ‘yan sanda da ke Owerri da ke jihar wanda suka kwashe sa’o’i uku ana yi.
Wata majiya tace:
“Yan bindiga da ake zargin ‘yan IPOB/ESN ne sun afka gidan yarin Owerri rike da makamai da abubuwa masu fashewa, hakan ya sa su ka saki ‘yan gidan yari da dama,” a cewar majiyar.
Daga baya, hukumar gidan yarin ta bayyana cewa fursunoni 1,844 ne suka tsere.
Daga bisani shugaban kasa ya tura jami’an tsaro binciko su sannan aka bayar da umarnin su koma ko kuma su fuskanci hukunci mai tsanani.
Banka wa Ofishin DSS wuta a Anambra
Har ila yau harin da ‘yan bindiga suka kai ofishin DSS da ke Nnewi a jihar Anambra ya razanar.
An ga yadda ‘yan bindigan suka kai farmaki a mota kirar SUV wanda da farko suka fara sintiri a wurin kafin su wuce.
Lamarin ya faru da makwanni kadan aka yi zaben gwamnonin jihar a ranar 6 ga watan Nuwamba.
Harin da ‘yan bindiga suka kai ofisoshin ‘yan sanda a fiye da jihohi 10
A ranar 21 ga watan Afirilu, ‘yan bindiga sun kai farmaki ofishin ‘yan sanda na Adani da ke karamar hukumar Uzo-Uwani a jihar Enugu.
‘Yan bindigan sun afka da misalin karfe 2:30 na dare inda suka halaka wasu ‘yan sanda sannan suka banka wa ofishin wuta.
A watan Mayu, wasu ‘yan bindiga sun babbaka ofisoshin ‘yan wuta a jihar Ribas. A nan suka halaka sojoji 7.
A watan Mayun dai wasu ‘yan daba sun kona ofishin ‘yan sanda na Izombe da ke karamar hukumar Oguta a jihar Imo.
Ba a yi sa’o’i 24 ba da ‘yan bindiga suka banka wa kotun majistare, ofishin ‘yan sanda da wata babbar kotu har da asibiti da ke Atta, karamar hukumar Njaba wuta ba a jihar. ‘Yan sanda 4 suka rasa rayukansu sakamakon harin.
A Oktoba, gwamnatin tarayya ta ce an babbaka ofisoshin ‘yan sanda 164 a yankin kudu maso gabas.
Fiye da fursinoni 500 sun tsere bayan kai farmaki gidan yarin Oyo
A Oktoba, ‘yan bindiga suka kai farmaki gidan gyaran hali da ke Abolongo, jihar Oyo inda su ka saki ‘yan gidan yari.
Wata majiya ta shaida wa The Cable cewa ‘yan bindiga cewa da misalin karfe 10pm ‘yan bindigan suka kai harin.
‘Yan gidan yarin guda 575 ne suka tsere sakamakon harin.
Rauf Aregbesola, ministan harkokin cikin gida ya shaida cewa ‘yan gidan yari 446 ne suka tsere daga gidan gyaran halin Abolongo amma duk an kama su.
A watan Nuwamba Aregbesola ya ce ‘yan gidan gyaran hali 3,906 ne suka tsere daga gidan yarin tun daga 2020 zuwa yanzu.
Asali: Legit.ng