Rashin tsaro: Ganduje ya ziyarci fadar Buhari, ya ce gwamnoni suna bukatar taimako

Rashin tsaro: Ganduje ya ziyarci fadar Buhari, ya ce gwamnoni suna bukatar taimako

  • Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya kai wa shugaban kasa Buhari ziyara kan tabarbarewar tsaro a fadin kasar nan
  • Ganduje ya koka kan yadda dajikan kasar nan a halin yanzu suke kunshe da 'yan bindiga, 'yan ta'adda, masu garkuwa da mutane da 'yan fashi
  • Ya ce gwamnonin kasar nan da shugabannin kananan hukumomi suna bukatar taimakon shugaban kasa Buhari domin shawo kan matsalar
  • Ganduje ya yi kira ga gwamnati da ta kafa sansanonin horar da jami'an tsaro cikin dajika, hakan zai taimaka wurin dakile lamurran ta'addanci

Aso Villa, Abuja - Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya ce kusan dukkan dajikan da je fadin kasar nan a yanzu kunshe suke da 'yan ta'adda, 'yan fashi da makamai, 'yan bindiga da sauran miyagun.

Kara karanta wannan

Bayan farmakin ISWAP a Borno, Buhari yace ana matakin karshe na yaki da 'yan ta'adda

Daily Trust ta ruwaito cewa, gwamnan ya samar da hakan ne yayin jawabi ga manema labaran gidan gwamnati bayan ganawar sirri da yayi da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadarsa da ke Abuja a ranar Juma'a.

Rashin tsaro: Ganduje ya ziyarci fadar Buhari, ya ce gwamnoni suna bukatar taimako
Rashin tsaro: Ganduje ya ziyarci fadar Buhari, ya ce gwamnoni suna bukatar taimako. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Ya kwatanta kalubalen tsaron da kasar nan ke ciki da abu mara dadi kuma ya yi kira ga shugaban kasa da ya taimaka wa gwamnonin, TheCable ta ruwaito.

Ya kara da bukatar a samar da sansanin horar da sojoji a dajin da ke tsakanin jihohin Kano, Kaduna, Bauchi da Filato domin duba al'amuran ta'addanci.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce, "Da farko dai, na zo in ga shugaban kasa ne kuma in mishi bayani game da halin da tsaron Kano ke ciki. Akwai kalubale a dukkan kasar nan na tsaro kuma abun takaici ne. Amma mun yarda cewa shugaban kasa yana yin duk abinda ya dace tare da masu ruwa da tsaki domin shawo kan lamarin."

Kara karanta wannan

Gwamna Sule ya sha alwashin kamo wadanda suka kashe manoma da makiyaya a Nasarawa

"Muna bukatar taimako, kusan kowa, ballantana gwamnoni da shugabannin kananan hukumomi. Mun lura da halin da tsaron kasar ke ciki, yanzu dajikanmu ne manyan matsaloli saboda su ke dauke da 'yan bindiga, 'yan ta'adda, masu fashi da makami.
"A Kano, mun dauka wasu matakai. Muna da manyan dajika biyu, dajin Falgore da ke da iyakoki da Kano, Kaduna da Bauchi kuma na shi da nisa da Filato. A wannan dajin mun samar da wurin horar da sojoji tare da hadin guiwar rundunar sojin Najeriya.
"Toh kuwa hakan ya taimaka wurin dakile lamurran 'yan bindiga. Na bukaci shugaban kasa da ya samar da wata ma'aikatar a cikin daji ta yadda za mu kwace dajikanmu.
"Hakazalika, mun kirkiro da fasaha a cikin dajin, daga ofishin DSS na jihar Kano da kuma kwamishinan 'yan sanda da ofishina, muna iya ganin abinda ke faruwa a dajin. Akwai kuma sadarwa yadda ya dace tsakanin DSS da 'yan sanda tare da wadanda ke kula da dajin."

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Shugaba Buhari ya tura wasika ga majalisa kan kudirin gyara kundin zabe

Sheikh Jingir ya magantu kan karuwar rashin tsaro, ya aike wa 'yan Najeriya muhimmin sako

A wani labari na daban, shugaban kungiyar Jama’atu Izalatu Bida’a Waikamatul Sunnah (JIBWIS), na kasa, Sheikh Muhammad Sani Yahaya Jingir, ya yi kira ga 'yan Najeriya da su tashi kai hade tare da kare kansu daga farmakin 'yan bindiga, masu garkuwa da mutane da kuma duk wasu 'yan ta'adda da ke rikita yankin arewacin Najeriya.

Daily Trust ta ruwaito cewa, ya sanar da manema labarai hakan ne a yayin bude gasar karatun Qur'ani na mako daya wanda kungiyar ta shirya a Dutse da ke jihar Jigawa a ranar Lahadi.

Malamin wanda ya koka da hauhawar rashin tsaro, garkuwa da mutane, fashi da makami da sauran nau'ikan rashin tsaro, ya bayyana cewa hanya daya tak ta shawo kan matsalar shi ne hada kai tare da tunkarar 'yan ta'addan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng