'Yan ta'adda za su gane kurensu: Kayan yaƙin da na siyo daga Amurka sun fara isowa, Buhari

'Yan ta'adda za su gane kurensu: Kayan yaƙin da na siyo daga Amurka sun fara isowa, Buhari

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya lashi takobi akan ci gaba da daukar matakai tsaurara na yaki da ‘yan bindigan da su ka addabi yankin arewa maso yamma
  • Buhari ya yi wannan furucin ne a ranar Alhamis yayin kaddamar da cibiyar ilimi ta Muhammadu Indimi a jami’ar Maiduguri da ke jihar Borno
  • Ya bayyana yadda yanzu haka kayan yaki da manyan makamai su ka fara isowa Najeriya daga Amurka don yaki da ‘yan ta’addan da su ka addabi kasa

Jihar Borno - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce jami’an tsaro za su ci gaba da yaki da ‘yan ta’addan da suka addabi yankin arewa maso yamma.

NewsWireNGR ta ruwaito Buhari ya bayyana hakan ne yayin kaddamar da cibiyar ilimi ta Muhammad Indimi a jami’ar Maiduguri da ke jihar Borno.

Kara karanta wannan

Shehun Borno: Tsaro ya inganta kwarai a Jihar Borno karkashin mulkin Buhari

'Yan ta'adda za su gane kurensu: Kayan yaƙin da na siyo daga Amurka sun fara isowa, Buhari
Buhari ya ce makamai da ya siyo domin yakar yan ta'adda sun fara isowa daga Amurka. Hoto: Fadar Shugaban Kasa
Asali: Facebook

Kamar yadda yace:

“Har jiragen yaki, helikwafta da ababen hawa na yaki sun fara isowa daga Amurka kuma zamu mike tsaye don yaki da su (‘yan bindiga) kamar yadda muka nema.”

Shugaban kasar ya bayyana murnarsa akan gyaruwar tsaron arewa maso gabas

Shugaba Buhari ya nuna farin cikinsa akan yadda tsaro ya gyaru a arewa maso gabashin kasar nan inda yace an dade ana kuka da ‘yan bindiga.

A cewarsa:

“Mutanen da su ke ta satar dukiyoyin jama’a ne suke ta halaka jama’a wuri-wuri yanzu haka. Me yasa hakan ke faruwa?”

Shugaban kasa ya bukaci ‘yan Najeriya da su yi alkalanci akan yadda yanzu kasa take da kuma yadda asali ya same ta sanda ya hau mulki, NewsWireNGR ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Babu sauran sassauci tsakanin mu da yan bindiga, musamman a arewa, Shugaba Buhari

A cewarsa:

“Yankin kudu-kudu sun samu ci gaba mai tarin yawa. A baya ana ta fasa rijiyoyin mai har ta kai ga ko kifaye ba sa iya yawo a cikin ruwa sannan mutane ba sa iya noma duk da kasancewar akwai manoma da masu kiwon kifi da yawa a kudu, yanzu duk an gyara.
“Yanzu babbar matsalar shi ne yankin arewa maso yamma shi ne yadda mutane masu al’ada guda da yare guda su ke addabar junayensu.
“Ina so ‘yan Najeriya su sanar da wadanda ba su sani ba cewa a Afrika, kasar mu ce mafi girma, daukaka da arziki. Mu yi amfani da baiwar da Ubangiji ya bamu don taimakon kasar mu.”

Shugaban kasa ya ce zai sauka daga mulki nan da watanni 17

Ya yi rantsuwa da Al’Qur’ani mai girma inda ya ce zai jajirce wurin bunkasa kasa cikin watanni 17 da su ka rage masa a karagar mulki.

Kara karanta wannan

Ka Samar Da Tsaro a Najeriya Ko Ka Yi Murabus, PDP Ta Fada Wa Buhari

Buhari ya ce zai sauka daga mulki kuma yana fatan duk wanda zai maye gurbinsa ya daura daga inda ya tsaya kuma ya bayar da isasshen tsaro.

Shugaban kasa ya ce yanzu ba ta man fetur ake yi ba duk da dai an gano cewa akwai mai a jihar Bauchi da kuma Gombe, wanda hakan zai kawo daidaito a batun mai a kasar nan.

Ya ce ya kamata cikin gaggawa a samar da matatun mai don kowa ya more. Ya ce idan hakan ta kammala ya tabbatar ‘yan Najeriya zasu yi alkalanci su fadi idan yadda ya samu kasar nan haka ya bar ta.

Ya ce yayi yaki da rashawa tun farkon hawan sa mulki

Ya bayyana yadda daga hawan sa mulki ya fara yaki da rashawa tun daga kananu har manyan mutane. An yi bincike akan kan gwamnoni, ministoci, kwamishinoni da sauran mutane.

Daga karshe Buhari ya yi godiya ga Ubangijin da ya ba damar mulkar Najeriya har sau biyu kuma ya ce ya kamata ‘yan Najeriya su jajirce wurin ciyar da kasar nan gaba.

Kara karanta wannan

Rashin 'Tarbiyya' Ne Yi Wa Shugaba Buhari Mummunan Addua'a, Tsohon Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa

Buhari: Da zarar na kammala wa'adin mulki na zan koma gona ta a Daura in tare

A wani labarin, Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce ya na da kudirin komawa gonarsa ta Daura, mahaifarsa da ke jihar Katsina, Daily Trust ta ruwaito.

Shugaban kasa ya furta hakan ne a Istanbul, kasar Turkiyya inda aka shirya masa bikin zagayowar ranar haihuwarsa ba tare da saninsa ba a ofishin jakadancin Najeriya da ke kasar.

Buhari ya na kasar Turkiyya yanzu hakan don halartar wani taro inda har ranar haihuwarsa ta zagayo, ya cika shekaru 79 kenan a ranar Juma’a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164