Yanzu-Yanzu: Bututun Man Fetur Ya Sake Kama Wa Da Wuta a Legas

Yanzu-Yanzu: Bututun Man Fetur Ya Sake Kama Wa Da Wuta a Legas

  • Bututun man fetur na hukumar NNPC ta sake yin gobara a Legas a Isale Odo, LASU Road, Egbeda, a unguwar Alimosho
  • Wasu ganau a yankin sun bayyana cewa gobarar ta faru ne sakamakon wayoyin wutar lantarki da suka fadi a kasa suka rika fitar da tartatsin wuta
  • Sai dai tuni 'yan kwana-kwana, jami'an NNPC, jami'an tsaro, da jami'an hukumar tsaro da NSCDC sun isa wurin domin kashe gobarar

Jihar Legas - Wata gobara da ta auku a safiyar ranar Juma'a, 24 ga watan Disamba ta sha bututun man fetur na Hukumar Tace Man Fetur ta Najeriya, NNPC, Vangaurd ta ruwaito.

Jami'an hukumar NNPC, jami'an tsaro, 'yan kwana-kwana da jami'an hukumar tsaro da NSCDC tuni sun isa wurin domin taimaka wa kashe gobarar.

Kara karanta wannan

Yadda Gwamnoni 6 suka hana Majalisa juyawa Shugaban kasa baya a kan kudirin gyara zabe

Yanzu-Yanzu: Bututun Man Fetur Ya Sake Kama Wa Da Wuta a Legas
Bututun man fetur ta sake yin gobara a Legas. Hoto: The Nation
Asali: UGC

An gano cewa gobarar na bututun man fetur wanda ba barazana bane ga al'umma ya faru ne a Isale Odo, LASU Road, Egbeda, a unguwar Alimosho a Legas.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewar ganau, wayoyin wutar lantarki da suka fadi a kasa ne suka yi tartatsin wuta a unguwar hakan yasa gobarar ta tashi saboda man fetur da ya zuba a kasa a unguwar har ta kai ga bututun man fetur din, rahoton Vanguard.

Masu satar man fetur sun saba zuwa yankin domin fasa bututun mai su yi sata.

Martanin shugaban 'yan kwana-kwana ne Legas

Shugaban hukumar kashe gobara da ceto al'umma na Legas, Mrs Adeseye Margret, wacce ta tabbatar da afkuwar lamarin misalin karfe 8.30 na safe ta ce:

"Muna sane da afkuwar gobarar kuma jami'an mu na can a Baruwa inda abin ya faru don kashe wutar."

Kara karanta wannan

Wanda ya yi wa Buhari Minista a 1984 ya kawo shawarwarin yadda za a magance rashin tsaro

Shugaban yan kwana-kwanan, wacce ba ta iya fadan ainihin musababbin gobarar ba ta ce jami'an ta suna gudanar da cikakken bincike don gano sanadin afkuwar gobarar.

Bauchi: Gobara ta lakume babban kasuwar kayan abinci, an yi asarar kayan miliyoyin naira

A wani labarin, mummunar gobara ta afka shaguna cike da kayan abinci makil masu kimar miliyoyi a wani bangare na sananniyar kasuwar kayan abinci ta Muda Lawal da ke jihar, Vanguard ta ruwaito.

An gano yadda wutar ta fara ruruwa da tsakar daren Laraba wacce ta ci gaba da ci har safiyar Alhamis inda ta janyo mummunar asarar kafin jama’a da taimakon ‘yan kwana-kwana su kashe wutar.

Duk da dai ba a gano sababin wutar ba, amma ganau sun ce daga wani shago wanda danyun kayan abinci su ke cikinshi ta fara bayan an kawo wutar lantarki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164