Allah ya tona asirin mai kaiwa yan bindiga muggan makamai a jihar Katsina

Allah ya tona asirin mai kaiwa yan bindiga muggan makamai a jihar Katsina

  • Rundunar yan sanda ta samu nasarar cafke wani Mamuda a Katsina bisa zargin kaiwa yan bindiga makamai
  • Kakakin yan sandan Katsina, SP Gambo Isa, yace an kama mutumin ne da bindigu, yana kan hanyar kai su Zamfara
  • Mutumin ya amsa laifinsa tare da bayyana adadin makudan kuɗaɗen da yake samu duk bindiga ɗaya

Katsina - Rundunar yan sanda reshen jihar Katsina ta bayyana cewa ta kama wani ɗan shekara 45, Sani Mamuda, da zargin samarwa yan ta'adda bindigu da alburusai Katsina da Zamfara.

Kakakin rundunar yan sandan Katsina, SP Gambo Isa, shine ya bayyana haka yayin da yake shigar da wanda ake zargin ranar Alhamis.

Vanguard ta rahoto cewa yan sanda sun damke wanda ake zargin ne yayin da yake kan hanyar zuwa Zamfara domin kai bindigun AK-47, da kuma Magazine cike da alburusai.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Sake Tare Motocci a Hanyar Kaduna-Birnin Gwari, Sun Bindige Mutane 6, Sun Sace Da Dama

Yan sanda
Allah ya tona asirin mai kaiwa yan bindiga muggan makamai a jihar Katsina Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Kakakin yan sandan ya ƙara da cewa wanda ake zargin ya boye bindigun da aka kama shi da su karkashin kujerar zama a motar da yake tuƙa wa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yace:

"A ranar 22 ga watan Disamba da misalin ƙarfe 7:30 na safe, DPO na caji ofis ɗin Kurfi da tawagarsa suka damke Mamuda ɗan asalin ƙaramar hukumar Birnin Magaji, jihar Zamfara."
"Mamuda gawurtaccen ɗan bindiga ne dake kaiwa yan ta'adda makamai a dajin jihohin Zamfara da Katsina, kuma ya shiga hannu a kan hanyar Kurfi-Batsari yayin da yake hanyar zuwa Zamfara daga Katsina."
"Mamuda ya amsa laifinsa yace ya siyo bindigun a dajin Mashi, hannun Masa'idu da Abdullahi, waɗan da har yanzun ba su shiga hannu ba."

Wane mataki yan sanda suka ɗauka?

Kakakin yan sandan yace yanzun jami'ai na kan bincike kan mutumin, kuma da zaran sun kammala za'a gurfanar da shi gaban kotu.

Kara karanta wannan

Ba gudu ba ja da baya sai mun murkushe yan bindiga a arewa da izinin Allah, Gwamna

Da yake amsa tambayoyi, Mamuda ya amsa laifinsa cewa yana kaiwa wasu yan bindiga makamai a jihar Zamfara.

Ya kuma kara da cewa yana samun ribar kudi tsakanin N50,000 zuwa N80,000 a duk bindiga ɗaya da ya siyar.

A wani labarin kuma Yan bindiga sun kashe dan Bijilanti, sun yi awon gaba da DSS a Abuja

Wasu tsagerun yan bindiga sun sace jami'in hukumar yan sanda ta farin kaya (DSS) a babban birnin tarayya Abuja.

Rahoto ya nuna cewa maharan sun kashe wani jami'in sa'kai ɗan bijilanti guda ɗaya yayin harin na ranar Asabar da daddare.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262