'Yan bindiga sun sheke mutum 7 a kusa da matsayar sojoji, sun sace wasu a Katsina da Kaduna

'Yan bindiga sun sheke mutum 7 a kusa da matsayar sojoji, sun sace wasu a Katsina da Kaduna

  • 'Yan biindiga sun halaka a kalla rayuka 7 a karamar hukumar Faskari ta jihar Katsina a farmakin da suka kai musu kusa da matsayar sojoji
  • Dan majalisa mai wakiltar mazabar Faskari kuma kakakin majalisar jihar Katsina, Shehu Tafoki, ya tabbatar wa da manema labarai hakan
  • A ranar Laraba kuwa, 'yan bindiga sun kai wa tawagar motocin 'yan kasuwa farmaki duk da 'yan sandan da ke musu rakiya a titin Kaduna zuwa Birnin Gwari

Katsina da Kaduna - A kalla rayuka bakwai ne aka kashe kusa da wurin zaman sojoji a karamar hukumar Faskari ta jihar Katsina.

'Yan bindigan da suka yi wannan aika-aikar su ne da alhakin sace wasu mutane wadanda suka hada da mata da kananan yara, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Har cikin masallaci, 'yan bindiga sun kutsa tare da sace masallata a Taraba

'Yan bindiga sun sheke mutum 7 a kusa da matsayar sojoji, sun sace wasu a Katsina da Kaduna
'Yan bindiga sun sheke mutum 7 a kusa da matsayar sojoji, sun sace wasu a Katsina da Kaduna. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Mataimakin kakakin majalisar jihar Katsina, Shehu Dalhatu Tafoki, wanda ke wakiltar mazabar Faskari a majlisar jihar, ya sanar da Daily Trust cewa wannan ya na daga cikin farmaki hudu da suka fuskanta a cikin mako daya.

Dan majalisar ya ce an kashe wasu mutanen yayin da aka sace wasu.

"Sun kai farmaki kauyen Kwakware inda suka sace mutane 17 wanda yawancinsu mata ne. Washegari sun tsare wani direba tare da kone shi a cikin motarsa.
"A ranar Talata kadai, sun kashe mutum bakwai tare da sace wasu biyar, wurin da suka yi barnar ba shi da nisa da matsayar sojoji," yace.

Hakazalika, a ranar Laraba, 'yan bindiga sun sace mutane masu tarin yawa a kan babban titin Kaduna zuwa Birnin Gwari bayan kai wa ayarin motocinsu ashirin farmaki wadanda 'yan sanda ke musu rakiya.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: Yan bindiga sun sake ƙona mutum kurmus a cikin mota a jihar Katsina

Cikakken bayanin lamarin da ya auku wurin karfe 11 na safen babu shi, amma an tattaro cewa da yawan wadanda aka sace 'yan kasuwa ne da ke kan hanyarsu ta zuwa Kano.

Wani shugaban yanki mai suna Muhammadu Umaru, ya sanar da Daily Trust cewa, hudu daga cikin makwabtansa duk suna hannun 'yan bindigan.

Kashe-kashe: Masu zanga-zanga sun mamaye manyan titunan Katsina, an bar fasinjoji a tsaka mai wuya

A wani labari na daban, fusatattun jama'ar jihar Katsina sun mamaye babban titin Funtua zuwa Sheme na jihar Katsina tare da hana ababen hawa wucewa a titin Funtua zuwa Gusau kan farmakin da 'yan bindiga ke kai musu.

Daily Trust ta ruwaito cewa, wani matafiyi mai suna Imam Abubakar, ya sanar da cewa matafiya suna nan dankare a wurin sun kasa yin gaba ko baya.

"Ga mu nan a wurin, ba zan iya fadin yawan ababen hawa da ke titin nan ba da masu zanga-zanga suka tare. A yanzu da muke magana, muna jin harbin bindigar 'yan sanda dasojoji wadanda aka turo yankin, amma masu zanga-zangar sun rufe titin suna kona tayoyi," yace.

Kara karanta wannan

Kashe-kashe: Masu zanga-zanga sun mamaye manyan titunan Katsina, an bar fasinjoji a tsaka mai wuya

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng