Kashe-kashe: Masu zanga-zanga sun mamaye manyan titunan Katsina, an bar fasinjoji a tsaka mai wuya
- Matafiya sun shiga mawuyacin hali sakamakon toshe babban titin Funtua zuwa Gusau da masu zanga-zanga suka yi a jihar Katsina
- Mazauna yankin sun fito kwansu da kwarkwatarsu inda suke zanga-zanga tare da kira ga gwamnati da ta dauka mataki kan rashin tsaro
- A cikin mako daya tak, 'yan bindiga sun kai farmaki yankin har sau biyar inda suka sace mutane biyar tare da halaka rayuka takwas
Funtua, Katsina - Fusatattun jama'ar jihar Katsina sun mamaye babban titin Funtua zuwa Sheme na jihar Katsina tare da hana ababen hawa wucewa a titin Funtua zuwa Gusau kan farmakin da 'yan bindiga ke kai musu.
Daily Trust ta ruwaito cewa, wani matafiyi mai suna Imam Abubakar, ya sanar da cewa matafiya suna nan dankare a wurin sun kasa yin gaba ko baya.
"Ga mu nan a wurin, ba zan iya fadin yawan ababen hawa da ke titin nan ba da masu zanga-zanga suka tare. A yanzu da muke magana, muna jin harbin bindigar 'yan sanda dasojoji wadanda aka turo yankin, amma masu zanga-zangar sun rufe titin suna kona tayoyi," yace.
'Yan bindiga sun kai farmaki wasu garuruwan da ke yankin inda suka kashe mutane takwas tare da sace wasu mata biyar, Daily Trust ta ruwaito.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Majiyoyi sun ce lamarin ya faru a karamar hukumar Faskari ta jihar a wani farmakin tsakar dare.
"A kauyen Kanon Haki, 'yan bindiga suna kashe mutane biyar yayin da suka kashe wasu mutum biyu a Unguwar Alhaji Ibrahim Maiwada," wata majiya ta ce.
Majiyar ta ce an kai wa kauyukan farmaki wurin karfe 9 na dare a ranar Litinin.
A yayin martani kan lamarin, mataimakin kakakin majalisar jihar Katsina, wanda shi ne dan majalisa mai wakiltar mazabar Faskari, ya ce kusan sau hudu aka samu farmakin 'yan bindiga a cikin satin nan a yankin.
Dan majalisar ya ce ya mika bukatar a gaban majalisa cikin lamurra masu bukatar daukin gaggawa, inda ya roki majalisar da ta yi kira da gwamnati da ta gaggauta kawo karshen ta'addanci a jihar.
Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Katsina, SP Gambo Isah, bai daga wayar da aka dinga kiransa ba kuma bai yi martani kan sakkon kar ta kwana da aka dinga aika masa.
Ku nuna tausayawar ku: ACF ta yi kira ga Buhari da gwamnoni da su ziyarci yankunan da ake ta'addanci
A wani labari na daban, kungiyar hadin kan Arewa, ACF ta yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnonin arewa akan nuna tausayi ga wadanda ta’addanci ya shafi yankinsu.
'Yan Bindiga Sun Sace Malaman Addinin Musulunci 2 Bayan Cika Cikinsu Da Teba Da Miya Da Matar Malamin Ta Dafa
TheCable ta ruwaito cewa, a wata takarda ta ranar Litinin wacce Emmanuel Yawe, Sakataren watsa labaran kungiyar ACF ya saki, ya yi alawadai da kisan mutane 38 na karamar hukumar Giwa da ke jihar Kaduna.
Kungiyar ta bukaci Buhari, gwamnoni da sauran shugabannin arewa da su yi iyakar kokarinsu wurin nuna kula ga wadanda lamarin ya ritsa da su, Daily Trust ta ruwaito haka.
Asali: Legit.ng