Malaman makaranta sun fara hada N500 kowannensu domin biyan kudin fansa ga 'yan bindiga
- Malaman makaranta a jihar Ekiti sun shiga tashin hankali yayin da aka sace abokiyar aikinsu kuma ake neman kudin fansa
- Rahotannin da muke samu sun bayyana cewa, malaman sun fara tara kudi domin karbo abokiyar aikin nasu
- Sai dai, kungiyar malamai ta NUT ta ce ba ta da hannu a lamarin tara kudin fansa da malaman aka ce suna yi a yanzu
Ekiti - Malamai a jihar Ekiti sun fara tara gudunmuwar Naira 500 kowannensu domin biyan kudin fansa ga masu garkuwa da mutanen da suka sace abokiyar aikinsu, Mrs Owoniyi.
An yi garkuwa da Owoniyi, malama a makarantar St. Pauls Primary School, Ikole Ekiti, a kan hanyar Ayobode-Ekiti, Daily Trust ta ruwaito.
Bayanai sun nuna cewa an sace malamar ne tare da wasu matafiya a ranar Lahadin da ta gabata, kuma masu garkuwa da mutanen sun nemi kudin fansa naira miliyan 50.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
An ce an sanar da neman tallafin kudin fansa ne a dandalin WhatsApp na malaman yankin Ikole.
Amma da aka tuntubi shugaban kungiyar malamai ta Najeriya (NUT) a jihar Ekiti Mista Oke Emmanuel ya ce wasu abokan aikin malamar ne suka yanke shawarar neman kudin ba kungiyar ba.
Yayin da yake tabbatar da rahoton sace mutanen, Emmanuel ya ce shugabar kungiyar ta NUT reshen Ikole, Mrs L. O. Longe, ta shaida masa cewa masu garkuwa da mutane suna neman kudin fansa naira miliyan 50.
Da yake wanke kungiyar NUT a hannu a lamarin, ya shaidawa jaridar Vanguard cewa:
"Wannan jita-jita ce, babu wanda ya nemi malaman Ekiti su ba da gudummawar kudi, ba gaskiya ba ne, labarin karya ne."
Sai dai jami’in hulda da jama’a na ‘yan sanda (PPRO) a Ekiti, ASP Sunday Abutu, a wata tattaunawa ta wayar tarho ya ce rundunar bata samu rahoton ba.
Wasu masu juna biyu sun haihu a kan tsaunuka garin gujewa 'yan bindiga
A wani labarin, wasu mata biyu masu juna biyu a jihar Neja sun haihu a kan wani tsauni a lokacin da suke kokarin tserewa hare-haren ‘yan bindiga a yankinsu.
Jaridar Nigerian Tribune ta rawaito cewa harin da aka kai a kauyen Kwimo da ke karamar hukumar Mariga ta jihar Neja ya sa daukacin al’ummar yankin tserewa don tsira da rayukansu.
A cewar wani ganau mai suna Usman Kwimo, ba zai iya tabbatar da halin lafiyar mata masu juna biyun da jariransu ba saboda ba su da kayan aikin jinya da ake bukata don kula da su.
Asali: Legit.ng