Da ɗuminsa: Hadimin Aisha Buhari ya magantu kan rade-raɗin samun juna biyun ta
- Babu gaskiya a lamarin, uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari, ba ta dauke da juna biyu in ji Sulaiman Haruna, hadimin ta
- Haruna ya karyata labaran da ke ta yawo na cewa Aisha na fama da laulayi, inda ya ce matar shugaban kasan lafiyar ta kalau
- Hotunan Aisha Buhari yayin da suka dira Najeriya daga kasar Turkiyya tare da shugaba Buhari sun dinga yawo inda ake cewa tana dauke da juna biyu
Sulaiman Haruna, wani hadimin Aisha Buhari, ya musanta rade-radin da ke ta yawo na cewa uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari, ta na dauke da juna biyu.
Legit.ng ta ga yadda aka dinga yada haotunan Aisha a kafafen sada zumuntar zamani inda ake ta cewa tana da ciki duba da yadda cikinta ya nuna a hotunan.
Hotunan uwargidan shugaban kasan yayin da suka dira babban birnin tarayya na Abuja daga kasar Turkiyya inda suka je taro tare da shugaban kasa Muhammadu Buhari, sun karade kafafen sada zumunta.
Ana tsaka da wannan rade-radin juna biyun, sai kuma aka fara rade-radin cewa Aisha ta na fama da laulayi.
Lafiyar Aisha Buhari kalau
Sai dai kuma, a wata tattaunawa da BBC Pidgin, Haruna ya musanta ikirarin inda ya ce uwargidan shugaban kasan lafiyar ta kalau.
Ya ce:
"Zan iya tabbatar muku da cewa lafiyar uwargidan shugaban kasa kalau. Babu wani ciwo da ke damun ta kuma ba ta dauke da juna biyu kamar yadda rahotanni ke ikirari.
"Wasu daga cikin rahotannin nan sun fito ne daga 'yan gutsiri tsoma wadanda ba su fatan alkhairi. Kun san yanzu, mutane sun kware wurin lalata hotunan jama'a."
Buhari ya aura Aisha a watan Disamban 1989 kuma Allah ya albarkaci auren da 'ya'ya biyar. A shekarar 2019, masoyan sun yi shagalin cikarsu shekaru talatin da aure.
Ana tsaka da jita-jitar tana da ciki Aisha Buhari ta umarci hadimanta su tafi hutu
A wani labari na daban, matar shugaban ƙasa, Aisha Muhammadu Buhari, ta umarci baki ɗaya ma'aikatan ofishinta su tafi hutu har sai sun ji daga gare ta.
Wannan na kunshe ne a wata sanarwa da uwar gidan shugaban ta fitar a shafinta na dandanlin sada zumunta Instagram (@aishambuhari).
Sanarwan na ɗauke da sa hannun babban mai baiwa shugaba Buhari Shawara kan harkokin lafiya, Dakta Mohammed Kamal, da haɗin guiwar ofishin matar shugaban ƙasa.
Asali: Legit.ng