Gwamna Sule ya sha alwashin kamo wadanda suka kashe manoma da makiyaya a Nasarawa
- Gwamna Abdullahi Sule na Jihar Nasarawa ya sha alwashin kamo wadanda suka yi wa manoma da fulani kisar gilla a jiharsa
- Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin wani taron tsaro da ya yi da jami'an tsaro, masu sarautun gargajiya da sauran masu ruwa da tsaki
- Gwamna Sule ya gargadi shugabannin al'umma su guji yin maganganu marasa tushe su mayar da hankali kan mayar da mutanensu garuruwansu
Nasarawa - Gwamnan Jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya sha alwashin kamo wadanda suka kashe makiyaya Fulani da manoman Tibi a jihar, da aka kashe a baya-bayan nan, domin su girbi abin da suka shuka, Daily Trust ta ruwaito.
Gwamnan ya yi wannan alwashin ne yayin taro da ya yi da shugabannin tsaro, masu sarautan gargajiya tare da shugabannin fulani da tibi a ranar Litinin a karamar hukumar Obi a jihar.
An yi taron ne na gaggawa a kokarin da gwamnatin ke yi domin dakile rikicin da ya barke a sassan kananan hukumomin Obi da Lafia a karshen makon da ya gabata, The Punch ta ruwaito.
Ya ce:
"Ana ta rasa rayyukar mutanen mu ba gaira ba dalili. Wannan zaluncin abin Allah-wadai ne kuma gwamnatin mu ba za ta amince da shi ba.
"Ina kira gare ku da ku zauna lafiya da juna kuma ku kauracewa masu neman tada rikici."
Ya bukaci shugabannin al'umma a yankin su dena furta maganganu marasa tushe, yana mai cewa hakan zai iya aike da sakon da ba a bukata a jihar da wajen jihar.
Jami'an tsaro ne suka dace su fadi adadin wadanda suka rasu
Game da adadin mutanen da aka kashe, Gwamnan ya ce jami'an tsaro da ke aikin dawo da zaman lafiya a yankin ne suka fi dace wa su gano adadin wadanda aka kashe.
Ya kara da cewa:
"A matsayin mu na gwamnati, za mu yi duk abu mai yiwuwa don gano abin da ya faru don kare afkuwar hakan a gaba.
"Za mu aike da kayan tallafi ga mutanen da suka rasa muhallinsu kuma gwamnati za ta yi aiki da dukkan masu ruwa da tsaki don ganin mutanensu sun koma cigaba da harkokinsu yadda suka saba."
An bindige manoma 45 har lahira a Nasarawa, wasu 5,000 sun rasa muhallinsu
Tunda farko, kun ji cewa kimanin manoma 45 ne aka kashe yayin da 27 suka jikkata sakamakon sabon hari da aka kai a kananan hukumomin Lafia, Obi da Awe a Jihar Nasarawa.
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa harin na farko da aka kai, tun safiyar ranar Juma'a ya cigaba har daren ranar Lahadi.
Wata majiya ta ce a kalla manoma 5,000 sun rasa muhallinsu a garuruwan sakamakon hare-haren da aka kai musu.
Asali: Legit.ng