'Karin Bayani: An bindige manoma 45 har lahira a Nasarawa, wasu 5,000 sun rasa muhallinsu

'Karin Bayani: An bindige manoma 45 har lahira a Nasarawa, wasu 5,000 sun rasa muhallinsu

  • Miyagun mahara da ba a tabbatar ko su wanene ba sun kai hari a garuruwan Nasarawa sun hallaka manoma 45 tare da jikkata 27
  • Mr Peter Ahemba, shugaban kungiyar yan kabilar tibi mazauna Nasarawa ya ce sun gano a kalla gawar mutum 20 kuma da wasu da dama da ba gansu ba
  • Rundunar yan sandan jihar Nasarawa ta bakin kakakinta Rahman Nansel ta ce ana zargin harin ramuwar gayya ne kuma sun tura jami'ansu

Jihar Nasarawa - Kimanin manoma 45 ne aka kashe yayin da 27 suka jikkata sakamakon sabon hari da aka kai a kananan hukumomin Lafia, Obi da Awe a Jihar Nasarawa.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa harin na farko da aka kai, tun safiyar ranar Juma'a ya cigaba har daren ranar Lahadi.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da 'yan bindiga sun sace sarkin gargajiya da malamin fada

Da Ɗumi-Ɗumi: An bindige manoma 45 har lahira a Nasarawa, wasu 5,000 sun rasa muhallinsu
An bindige manoma 45 har lahira a Nasarawa, wasu 27 sun jikkata. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Wata majiya ta ce a kalla manoma 5,000 sun rasa muhallinsu a garuruwan sakamakon hare-haren da aka kai musu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wasu daga cikin wadanda suka jikkata, suna nan a halin yanzu a asibitoci a kananan hukumomin Obi, Lafia da Awe ana basu kulawa.

Mun samu gawar yan uwan mu 20, Sarkin Kungiyar 'Yan Tibi

Shugaban kungiyar yan kabilar tibi mazauna jihar, Mr Peter Ahemba yayin hira da ya yi da wakilin Daily Trust ya ce sun gano a kalla gawar yan uwansu guda 20 a kananan hukumomin uku.

Ya ce garuwan da abin ya fi shafa sune Chabo, Daar, Tse-Udugh, Ayaakeke, Kyor-Chiha, Usual da Hagher.

Sauran sun hada da Joor, Angwan, Ayaba, Tyungu da Ugba.

Ya kara da cewa mazauna garuruwan sun bar gidajensu saboda tsoron sake kawo musu hari.

Kara karanta wannan

Innalillahi: 'Yan bindiga sun kai hari Kaduna, sun hallaka mutane tare da kone gonakai

Kalamansa:

"Fiye da mutane 5,000 sun rasa muhallinsu, sun yi hijira zuwa garuwan Obi da Agwatashi yayin da wasu suka tafi wurin yan uwansu a karamar hukumar Lafia.
"Kawo yanzu, mun gano gawarwaki fiye da 20 da taimakon jami'an tsaro na yan sanda da sojoji a Nasarawa.
"Akwai mutane da dama da ba a gansu ba kuma ba mu san ko suna raye ko kuma sun mutu ba."

Abin da yan sanda suka ce

Kakakin yan sandan jihar Nasarawa, ASP Rahman Nansel ya yi bayanin cewa an shigar da korafi a ranar Juma'a cewa yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kashe wani Umaru Idrisu na kauyen Gidan Washi.

Ya ce bayan hakan an tura jami'ai zuwa wurin inda aka dakko gawar aka kai asibiti don bincike kafin a bawa iyalansa su masa jana'iza irin ta musulmi.

Ya ce:

"Yayin da ake cigaba da bincike, ana zargin an kai harin ramuwar gayya a kauyen Hangara, a kananan hukumomin Lafia East da Lafia ya haura kauyen Kwayero na karamar hukumar Obi.

Kara karanta wannan

Hukumar Kwastam ta yi ram da kwantena cike da bindigogi da harsasai a Tin Can Legas

"Ga sunayen wadanda aka kai wa hari aka kashe su: Sani Dauda, Danjuma Liambee, Uloho Jerry, Shedrack Kente, Boniface John, Tersoo Clement, Gwanje Soja da Ayuba Ali; Yan sanda sun kai gawarsu asibiti."

Ya kara da cewa an tura tawagar yan sanda da sojoji domin su samar da zaman lafiya a yankin

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164