Karya kake mana, Hukumar DSS ta maida martani kan zargin da Sheikh Zakhzaky ya mata

Karya kake mana, Hukumar DSS ta maida martani kan zargin da Sheikh Zakhzaky ya mata

  • Hukumar tsaro DSS ta bayyana rashin jin daɗinta bisa zargin da Sheikh Zakzaky ya jingina mata na karkatar da wasu kudi
  • Hukumar tace bai dace malamin addini kamar Zakzaky ya fito ya na yin karya kuma dakansa ya nuna sha'awa kan yadda DSS ke tsare da shi
  • Shugaban kungiyar Shia ya zargi DSS da karkatar da wasu kudi da aka turo domin inganta kula da shi lokacin da yake tsare

Abuja - Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS), ranar Litinin, ta zargi shugaban kungiyar IMN, wacce aka fi sani da Shi'a, Ibrahim Zakzaky, da kirkirar karya ya jingina mata.

The Nation ta rahoto cewa hukumar ta musanta zargin da shehin malamin ya yi cewa ta karkatar da wasu kuɗaɗe da aka tura masa da matarsa yayin da suke tsare.

Kara karanta wannan

Masu gaskiya biyar da suka mayar da kudaden da suka tsinta ga masu shi a shekarar 2021

A wata fira da jaridar Punch, Malam Zakzaky, ya zargi DSS da wawure kudin alawus ɗinsu na wata-wata miliyan N4m yayin da suke tsare.

Zakzaky da DSS
Karya kake mana, Hukumar DSS ta maida martani kan zargin da Sheikh Zakhzaky ya mata Hoto: dubawa.org
Asali: UGC

Ya kuma zargi cewa hukumar DSS ta yi amfani da waɗan nan kuɗaɗe wajen kula da abincin jami'anta da kuma wasu kayayyaki na tsawon lokacin.

Martanin DSS

Amma kakakin DSS, Dakta Peter Afunanya, yace maganar malamin zuƙi ta malle ce da ya shirya domin bata wa hukumar suna.

Afunanya yace:

"Wannan tsagwaron ƙarya ce da aka shirya domin cutar da hukumar tsaro kamar DSS. Abun takaici ne mutum kamar shi (Zakzaky) ya zabi yin ƙarya. Da yuwuwar ya rasa basirar banbance gaskiya da ƙarya."
"DSS ba ta zaluntar waɗan da ake zargi. Yayin da ya tafi Indiya a shekarun baya, shi da kansa ya nemi ya dawo hannun jami'an DSS. Meyasa? saboda yana samun kulawa mai kyau a cewarsa."

Kara karanta wannan

Sheikh Jingir ya magantu kan karuwar rashin tsaro, ya aike wa 'yan Najeriya muhimmin sako

"Idan mutun yasan yana da kalubale a kotu, zai fi masa kyau ya maida hankali kan abin da ke damunsa, kuma a daina zargin DSS."

DSS na mutunta doka

Afunanya ya ƙara da cewa a kowane lokaci hukumar DSS na bin dokoki kuma tana samun jagoranci bisa doka da tsari.

"Daraktan DSS, Alhaji Yusuf Magaji Bichi, mutum ne mai mutunta doka da kuma saka demokaradiyya a harkokin jagorancinsa."

A wani labarin na daban kuma Jami'an yan sanda sun kama Sarki a Najeriya kan wani zargi

Jami'an rundunar yan sanda sun kama wani sarki a jihar Delta bisa zarginsa kan badakalar filaye a yankinsa.

Mutanen yankin musamman matasa sun shiga tashin hankali, yayin da suka fara yaɗa cewa wasu ne suka yi garkuwa da sarkin su.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel