Sheikh Jingir ya magantu kan karuwar rashin tsaro, ya aike wa 'yan Najeriya muhimmin sako
- Sheikh Muhammad Sani Yahaya Jingir, shugaban kungiyar JIBWIS a Najeriya, ya yi kira ga 'yan Najeriya da su tashi tsaye tare da hade kansu wurin bai wa kansu kariya
- Sheikh Jingir ya bayyana cewa, babbar matsalar 'yan Najerya shi ne tsoro, ta yaya yanki mai matasa sama da 2000 za su tsaya wasu 30 su kai musu farmaki
- Fitaccen malamin ya bukaci 'yan Najerya da su tashi tsaye tare da cewa cin kashin ya isa haka, hukumomi kuma su samarwa jami'an tsaro kayan aiki
Dutse, Jigawa - Shugaban kungiyar Jama’atu Izalatu Bida’a Waikamatul Sunnah (JIBWIS), na kasa, Sheikh Muhammad Sani Yahaya Jingir, ya yi kira ga 'yan Najeriya da su tashi kai hade tare da kare kansu daga farmakin 'yan bindiga, masu garkuwa da mutane da kuma duk wasu 'yan ta'adda da ke rikita yankin arewacin Najeriya.
Daily Trust ta ruwaito cewa, ya sanar da manema labarai hakan ne a yayin bude gasar karatun Qur'ani na mako daya wanda kungiyar ta shirya a Dutse da ke jihar Jigawa a ranar Lahadi.
Malamin wanda ya koka da hauhawar rashin tsaro, garkuwa da mutane, fashi da makami da sauran nau'ikan rashin tsaro, ya bayyana cewa hanya daya tak ta shawo kan matsalar shi ne hada kai tare da tunkarar 'yan ta'addan.
Ya buga misali da yadda wasu zakakuran 'yan Najeriya suka samu wannan nasarar a baya, Daily Trust ta ruwaito.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya kwatanta tsoro da babbar matsalar da ke assasa rashin tsaro da al'amuran 'yan bindiga a yankin arewacin kasar nan.
Ya dinga mamakin yadda yankin da ke da sama da matasa dubu biyu majiya karfi, har wasu talatin za su iya zuwa su addabe su.
Ya ce lokaci ya yi da 'yan Najeriya za su tashi tsaye su sanar da 'yan ta'addan cewa "ya isa haka".
Ya kara da kira ga wadanda ke da hakki a hukumance da su samar da kudin tsaro ga hukumomin tsaro domin tabbatar da sun sauke nauyinsu na bai wa rayukan jama'a da kadarori kariya.
Ya kara da jan kunnen hukumomin tsaron da su tabbatar da cewa sun yi amfani da kayayyakin da aka samar musu yadda ya dace.
Rashin tsaro: Shugaban JIBIWIS, Jingir yace Buhari ya fi Shugabannin baya
A wani labari na daban, shugaban kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’a Waikamatis Sunnah na kasa, Sheikh Sani Yahaya Jingir, ya yabi shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Malamin yana ganin duk da kalubalen da gwamnatin nan take fuskanta na tsaro, Muhammadu Buhari ya zarce sauran shugabannin da suka shude a baya.
Jaridar Daily Trust ta ce Sheikh Sani Yahaya Jingir ya bayyana wannan ne a wajen taron gasar Al-Qur’ani ‘musabaqa’ na kasa da aka shirya a garin Gombe.
Asali: Legit.ng