Alkali ya fallasa lauyan da tayi yunkurin ba shi cin hanci a Plateau
- Hon. Justice G. M Kamyal na babbar kotu ta 9 a West of Mines da ke Jos, jihar Filato ya fallasa wata ziyara da wata lauya ta kai masa
- Alkalin ya bayyana yadda bayan gabatar da shari’ar a gabansa, ana gobe zai saurari kara wata barista da wani suka je gidansa don kai masa kyautukan rashawa
- Don haka saboda hassalar da ya yi ya fasa sauraron karar, zai mayar da ragamar karar gaban babban Alkalin jihar don ya zabi wani alkalin na daban
Plateau - Hon. Justice G. M Kamyal na babbar kotu ta 9 na West of Mines da ke Jos, jihar Filato, ya fallasa yadda wata lauya ta yi yunkurin kai masa cin hanci akan wata shari’a da zai yi alkalanci.
Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, yayin bayar da labarin yadda lamarin ya auku a kotun ya bayyana yadda lauyan ta bukaci alfarma a kan kara mai lamba ta PLD/J602/2021 da ke tsakanin Gabriel Sunday Badung da wasu mutane 20 da Comr Samson Makima da wasu, inda alkalin ya bayyana mamakinsa akan ganin lauyar har gidansa da dare.
Lokacin da ya kamata a ci gaba da sauraron karar a ranar Talata, bayan lauyoyin sun gabatar da kawunansu gaban kotun, alkalin ya kada baki ya ce:
“Ina son sanar da lauyoyi da bangarorin da ke kotu akan cewa jiya da dare tsakarin 7 da 8, wata barista B. C. Awang (Mrs) ta zo har gidana tare da wani wanda ta ce sun zo gani na ne saboda wata shari’ar da zan yi alkalanci a kanta.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
“Sun zo tare har da kyautuka. Na shiga damuwa matsananciya saboda wannan ziyarar da su ka kai min. Na tambayesu dalilin da ya sa su ka kai min ziyarar saboda karar da aka gabatar gaba na.
“A cewar Barista B. C. Awang, sun kawo min ziyarar ne akan wata kara da aka gabatar gabana. Gaskiya ban ji dadin ziyarar ba, kuma rashin sanin aiki ne kuma gani nake yi sun kawo min ziyara ne don neman alfarma a wurina.
“Na yi matukar jin haushin ziyarar kuma hakan ya sa min rashin natsuwa dangane da shari’ar. Na ce wannan budaddiyar kotu ce kuma ina so in mayar da shari’ar hannun babban alkalin jihar don ya sake zaben wani alkalin da zai yi shari’ar.
“Saboda kada fushina akan ziyarar da suka kai gidana ya taba shari’ar da zan yi, don haka na mayar da shari’ar zuwa magatakardar kotun nan don a jira jin umarnin Hon. Ag, babban Alkalin jihar.”
Daily Trust ta ruwaito cewa, Alkali ya yanke wa lebura hukuncin dauri a gidan yari kan satar N51,000 a Plateau
A wani labari na daban, babbar kotun Jos da ke zama a Kasuwan Nama ta yanke wa wani lebura, El-Kanan Emmanuel hukuncin shekaru 5 akan satar N51,000.
NewsWireNGR ta tabbatar da cewa Alkalin, Lawal Suleiman ya yanke wa Emmanuel hukuncin bayan ya amsa laifukan sa na ta’addanci da sata sannan ya roki kotu ta sassauta masa hukunci.
Suleiman ya bai wa mai laifin zabin biyan tarar N20,000. Ya kuma umarce shi da ya biya N51,000 a matsayin kudin ya da sata har aka kawo korafin sa.
Asali: Legit.ng