Alkali ya yanke wa lebura hukuncin dauri a gidan yari kan satar N51,000 a Plateau

Alkali ya yanke wa lebura hukuncin dauri a gidan yari kan satar N51,000 a Plateau

  • Alkalin babbar kotun Jos da ke zama a Kasuwan Nama ta yanke wa wani lebura, El-Kanan Emmanuel shekaru 5 akan satar N51,000
  • Alkalin, Lawal Suleiman ta daure shi bayan ya amsa laifin satar da ya yi na ta’addanci sannan ya bukaci kotu ta sassauta ma sa
  • Alkalin ya ba Emmanuel zabin biyan tarar N20,000, sannan ya biya N51,000 a matsayin kudin da ya sata

Jihar Filato - Babbar kotun Jos da ke zama a Kasuwan Nama ta yanke wa wani lebura, El-Kanan Emmanuel hukuncin shekaru 5 akan satar N51,000.

NewsWireNGR ta tabbatar da cewa Alkalin, Lawal Suleiman ya yanke wa Emmanuel hukuncin bayan ya amsa laifukan sa na ta’addanci da sata sannan ya roki kotu ta sassauta masa hukunci.

Kara karanta wannan

Satar waya ta N80,000: Ɗan kasuwa ya shigar da ƙarar karuwa a kotun shari'a a Kaduna

Alkali ya yanke wa lebura hukuncin dauri a gidan yari kan satar N51,000 a Plateau
Kotu ta yanke wa lebura hukuncin dauri a gidan yari kan satar N51,000 a Plateau. Hoto: NewsWireNGR
Asali: Facebook

Kotu ta bai wa mai laifin zabin biyan tarar N20,000

Suleiman ya bai wa mai laifin zabin biyan tarar N20,000.

Ya kuma umarce shi da ya biya N51,000 a matsayin kudin ya da sata har aka kawo korafin sa.

Dan sanda mai gabatar da kara, Saja Ibrahim Gokwat ya sanar da kotu cewa wata Theresa Bala ce ta kawo karar a ofishin ‘yan sandan Mista Ali a ranar 17 ga watan Augusta.

A cewar sa Emmanuel ya balle gidan Bala ne inda ya sace N51,000.

Kamar yadda NewsWireNGR ta tabbatar, mai gabatar da karar ya ce yayin bincike mai laifin ya amsa laifin sa.

Dan sandan ya kara da cewa laifin ya ci karo da sashi na 212 da 213 na kundin tsarin jihar Filato na arewacin Najeriya.

Kara karanta wannan

2023: Fitaccen dan majalisar arewa ya bayyana dalilin da ya sa APC ke zawarcin Jonathan, ya yi magana akan kudirin Tinubu

Adamawa: Jarumin mai shago ya ragargaji ‘yan daba 2 da su ka yi kokarin fasa masa shago

A wani rahoton, kun ji wani mai shago, Mohammed Hamman Adama, ya nuna gwarzontakarsa bayan ya yi dambe da wasu yaran Shila yayin da su ka yi kokarin balle masa shagon sa da ke Sangere Bode a karamar hukumar Yola ta kudu a jihar Adamawa.

LIB ta ruwaito yadda aka tattaro bayanai akan wadanda ake zargin, Umar Sa’ad, mai shekaru 18 da Mohammed Idris, mai shekaru 20 suka lallaba shagon sa da misalin karfe 2:00 na daren 2 ga watan Satumban 2021 da addunan su, gudumomi, sanduna da sauran miyagun makamai.

Bayan isar su shagon har sun fara balle kofar don su samu nasarar yasar shagon. Su na kici-kicin balle kofa mai shagon ya ji kara ya fita cikin sauri.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164