Mawaki ya gwangwaje shugaban 'yan bindiga, Bello Turji, da wakar yabo da jinjina

Mawaki ya gwangwaje shugaban 'yan bindiga, Bello Turji, da wakar yabo da jinjina

  • Wani mawaki mai suna Adamu Ayuba ya gwangwaje hatsabibin shugaban 'yan bindiga, Bello Turji, da wakar yabo tare da kambamawa
  • A cikin wakar mai tsawon mintuna goma sha hudu, an ji mawakin ya na kiran Turji da jarumi kuma sadauki, duk da kuwa barnar da ya ke a arewa
  • Bello Turji dan asalin garin Shinkafi ne da ke jihar Zamfara kuma ya addabi jihohin Zamfara da Sokoto tare da wani sashi na Nijar da ta'addancinsa

Zamfara - Wata waka ta kwarzantawa tare da yaba wa fitaccen dan bindiga, Bello Turji, tana yawo a halin yanzu a arewacin Najeriya cikin mutanen da suke fama da cin zarafi tare da rashin kwanciyar hankalin da 'yan bindigan suke saka yankin.

Turji, wanda dan asalin garin Shinkafi ne daga jihar Zamfara, shi ne shugaban 'yan ta'addan da ke addabar jihohin Sokoto, Zamfara da wani sashi na jamhuriyar Nijar.

Kara karanta wannan

Dubun yan bindigan da suka kashe mutane a masallaci a jihar Neja ya cika

Mawaki ya gwangwaje shugaban 'yan bindiga, Bello Turji, da wakar yabo da jinjina
Mawaki ya gwangwaje shugaban 'yan bindiga, Bello Turji, da wakar yabo da jinjina. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

'Yan ta'addan ke da alhakin kisa da hana daruruwan jama'a sakat a yankin, Premium Times ta ruwaito.

Daya daga cikin mummunan al'amari shi ne kisan ranar 6 ga watan Disamban shekarar nan inda 'yan ta'addan suka kone mota cike da fasinjoji da ke kan hanyar su ta zuwa karamar hukumar Isa ta jihar Sokoto.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wakar mai tsayin kusan mintuna 14 an yi ta ne da Hausa kuma wani mutum mai suna Adamu Ayuba tare da wata muryar mace suna yaba wa Turji tare da kiran shi sadauki kuma jarumi.

Miyagun ayyukan Turji

A makon da ya gabata, Kungiyar Habaka yankunan Gobir (GCDA) ta hannun shugaban ta, Ibrahim Alhassan, ta rubuta budaddiyar wasika zuwa ga shugaban kasa Muhammadu Buhari kan halin da suke ciki, Premium Times ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Yanzu kam lokaci ya yi da ya kamata kowa ya nemi makami, gwamna Masari ya magantu

Kungiyar ta ce dan bindiga Turji ya kwace ikon gwamnatocin tarayya, jiha da na kananan hukumomi, ikon masarautar Sokoto, Shinkafi a jihar Zamfara da kuma hakimai da dagatai duk karkashinsa suke.

Kungiyar ta ce kananan hukumomin Sabon Birni, Goronyo da Isa da ke jihar Sokoto da karamar hukumar Shinkafi a jihar Zamfara duk karkashin ikon Turji suke inda dakarunsa ke garkuwa da mutane tare da fyade a lokutan da suka so.

"Ya na tare tituna, hargitsa kasuwa, kwace kayan abinci da duk wani abinda ya yi mishi kuma ya kashe duk wanda zai yi taurin kai," wasikar tace.
"Ya na korar dagatai kuma ya nada nashi. Ya na kallafa haraji a yankuna. Duk kauyen da bai biya haraji ba, Bello Turji na ziyartarsa da gaggawa kuma ya kai mummunan hari, ya kashe duk wanda ya kama, mata ko kananan yara duk daya ne.
"Daga cikin kauyukan da Turji ya hargitsa akwai Gajit, Lajinge, Tarah, Unguwar Lalle, Kurawa, Gangara da Garin Idi. A watan da ya gabata, Bello Turji ya kakkabe kauyen Garki mai nisan kilomita biyar daga Sabon Birni kuma ya kashe mutum 80 a dare daya.

Kara karanta wannan

Akwai Abin Tsoro Da Takaici A Kasar Nan, Malamai dai sun yi nasu kokarin: Dr Rabiu Rijiyar Lemo

"A ranar Talatar makon da ya gabata, wannan dan ta'addan ya aiwatar da muguntar da ta girgiza duniya. Yaran sa sun kone mutane a cikin mota kurmus yayin da suke hanyar barin Sabon Birni.
"Babu noma, babu tafiye-tafiye kuma babu kasuwanni. Babbar matsalar da muke fuskanta a yau shi ne, kana cikin gidan ka 'yan ta'adda za su shiga su ci zarafin ka gaban iyalin ka. Dukkan yankunan nan da na fada an saka musu haraji kuma suna biya. Ko da kuwa an biya, babu zaman lafiya," kungiyar tace a budaddiyar wasikar.

Jama'a sun kushe lamarin

Abba Ya'u, mazaunin Kano, ya kwatanta wakar da abun mamaki kamar yadda ya ji ana kambama Turji, ya kara da cewa "wannan ya bayyana wahalar yaki da ta'addancin a yankin.
"Ta yaya mutum mai tunani zai rera wa dan ta'addan da ke tada bala'i, tare da kashe mutane wakar yabo? A gaskiya mutanenmu ba su da hankali.

Kara karanta wannan

Harin 'Yan Bindiga: 'Yan Sanda Sun Tabbatar Da Mutuwar Mutum 23 a Sokoto

"Wannan ta'addancin zai zo karshe ne idan mutane suna so ya zo karshe saboda yankuna ya shafa," Ya'u yace.

Wani mazaunin Kano mai suna Abdullahi Kausi, ya ce gwamnati ta na daukar lamarin nan kamar wasan yara, wanda yace hakan ne yasa wasu mazauna yankunan suka fara goyon bayan 'yan bindigan saboda son samun kariya.

Kausi ya ce wakar da aka yi wa Turji, fitaccen makashin jama'a, ya nuna cewa matsalar ta yanki ce kuma akwai bukatar mutane su tashi tsaye wurin yaki da ta'addanci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng