Da duminsa: An sake samun gawar wani basarake da aka sace a Imo
- Mutanen yankin Ihitte Ihube da ke karamar hukumar Okigwe a jihar Imo sun wayi gari da mummunan al'amarin mutuwar basarake Ogbu
- Wasu miyagu sun shiga har fadar basaraken Imo inda suka sace shi amma daga bisani sai suka kashe shi a gaban wanda suka sace su tare
- Jami'an 'yan sanda sun samu gawar basarake a wani rami, duk da dai ba wannan bane karo na farko da hakan ta taba faruwa kan basarake ba
Imo - Jama'ar yankin Ihitte Ihube da ke karamar hukumar Okigwe ta jihar Imo sun shiga cikin jimami da dimuwa bayan samun gawar basarake Eze Pau Ogbu da aka yi.
A ranar Lahadi, an sace Eze Ogbu da wani shugaban matasa an sace su bayan an kone fadarsa da wasu ababen hawa, Daily Trust ta ruwaito hakan.
Amma an samo gawarsa a ranar Laraba kuma an aika da ita fadarsa yayin da ake shirin birne shi, SaharReporters ta ruwaito.
An tattaro cewa, an sace wani basarake mai sun Acho Ndukwe tare da Ogbu kuma shi ne ya sanar da cewa wadanda suka sace su sun kashe Ogbu.
Ndukwe ya bayyana cewa, wadanda suka sace su sun kashe Eze Ogbu a gabansa.
Jami'an tsaro sun koma har sansanin 'yan ta'addan wadanda 'yan asalin yankin ne inda suka iya ganin gawar basaraken a wani rami.
Ogbu da Ndukwe an sace su a ranar Lahadi inda aka banka wa fadarsu da ababen hawansu wuta.
An samu nasarar ceto Ndukwe a ranar Litinin bayan jami'an tsaro sun kai samame sansaninsu da ke kananan hukumomin Orsu da Ihiala a jihar Anambra.
An tsinta gawar wani basarake gargajiya a makon da ya gabata bayan an sace shi da kwanaki.
An tsinci gawar jami'in kwastam da miyagu suka yi garkuwa da shi
A wani labari na daban, an tsinci gawar jami'in hukumar kwastam da ake sace a jihar Ogun a ranar Talata da ta gabata, Daily Trust ta wallafa.
Wasu miyagu da ake zargin 'yan sumogal ne suka yi wa jami'an kwanton bauna yayin da suka fita sintiri a karamar hukumar Yewa ta kudu da ke jihar kuma suka sace jami'ai biyu.
An tsinta gawar daya daga cikin jami'an a wani rafi kusa da kauyen Fagbohun da ke karamar hukumar a ranar Laraba.
Asali: Legit.ng