Hoton magidanci da ya jagoranci garkuwa da matarsa tare da halaka ta don ya gaji dukiyarta
- Rundunar ‘yan sanda masu binciken sirri sun kama wasu mutane hudu da ake zargin su na da alaka da halaka Marigayiya Nneka Nwanyi-Sunday Emeh Kalu
- Da farko an neme ta an rasa ne a ranar 29 ga watan Augustan 2021 a anguwar Ngugworo da ke Nguzu Edda a karamar hukumar Afikpo ta kudu da ke jihar Ebonyi
- Cikin wadanda ake zargin akwai Iren Ifeanyi Mbah, Igwe Anya Chima, Okorie Okam da Emeh Kalu, wanda shi ne mijin marigayiyar kuma babban abin zargin
Ebonyi - Rundunar ‘yan sanda masu binciken sirri, IRT sun kama wasu mutane hudu da ake zargin su na da alhakin sata da kuma kisan gillar Marigayiya Mrs Nneka Nwanyi- Sunday Emeh Kalu, LIB ta ruwaito.
A ranar 29 ga watan Augustan 2021 ne aka nemi marigayiyar aka rasa a anguwar Ngugworo da ke Nguzu Edda cikin Afikpo ta kudu a jihar Ebonyi, daga bisani aka tsinci gawarta a gonar rogo.
A wata takarda wacce LIB ta ruwaito Kakakin rundunar ‘yan sanda, Frank Mba ya bayyana cewa ana zargin Irem Ifeanyi Mbah, Igwe Anya Chima, Okorie Okam da Emeh Kalu, wanda shi ne mijin marigayiyar kuma babban abin zargi.
An kama su ne bayan wasu mutane sun kai korafi akan tsintar gawar matar
Wadanda ake zargin shekarun haihuwarsu tsakanin 25 ne zuwa 40 kuma duk ‘yan kauyen Nguzu Edda ne da ke karamar hukumar Afikpo ta kudu a jihar Ebonyi.
A cewar Mba, sun fara bincike ne bayan mutanen Ngugworo, wani gari a Jihar Ebonyi da ya ke da iyaka da jihar Abia, sun kai korafi akan tsintar gawar mamaciyar a rube cikin yankinsu.
A cewarsa, nan da nan ‘yan sanda su ka fara bincike wanda dalilin haka su ka kama mutane hudun da ake zargi su na da alaka da laifin.
Ana zargin mijinta da halaka ta don ya yi wadaka da dukiyarta
Kamar yadda takardar tazo:
“Binciken rundunar ‘yan sanda ya bayyana cewa Emeh Kalu, mijin marigayiyar, ya yi aika-aikar ne don ya gaji tarin dukiyoyinta wadanda su ka hada da filaye, gidaje, kasuwanci da kuma tarin kudin da ke asusuwan bankinta.
“Hakan ya sa ya gayyaci wasu mutane biyar don su taya shi garkuwa da matarsa bayan ya yaudareta ta hanyar kiranta zuwa wani wuri don amsar kayan cefanen gida.
“Binciken ya kara nuna yadda su ka azabtar da ita har ta rasa ranta bayan ta bayar da bayanai akan duk inda dukiyoyinta su ke da takardu. Har yanzu ana ci gaba da tuhumar wadanda ake zargin don kammala bincike.”
Kakakin rundunar ‘yan sanda ya ce za a gurfanar da su gaban kotu
Yayin da kakakin ya yi wa danginta ta’aziyya akan wannan mummunan rashin, ya bukace su da su kasance masu kaunar juna kuma su samar da bayanai wadanda za su taimaka wa ‘yan sanda wurin dakatar da duk wata baraka makamanciyar wannan.
Mba ya kara da sanar da cewa za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu idan bincike ya kammala.
Asali: Legit.ng