Da Dumi-Dumi: Kasafin kudin shekarar 2022 ya samu koma baya a Majalisa
- Majalisar dattawan tarayyan Najeriya ta sha alwashin gama aiki kan kasafin kudin shekarar 2022 a watan Disamba
- Sai dai a jadawalin da majlisar ta tsara zata amince da kasafin ranar Alhamis ta wannan makon amma an samu matsala
- Har yanzun hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) da hukumar kidaya ta ƙasa (NPC) ba su kare na su kasafin ba
Abuja - Yan majalisun tarayya ba zasu samu damar amincewa da kasafin kudin Najeriya na shekarar 2022 ba, The Nation ta rahoto ranar Laraba.
A jadawalin kare kasafin kudin da majalisar dattawa ta tsara, za'a gabatar da kasafin kudin ranar Talata da Laraba domin amincewa da shi ranar Alhamis.
Sai dai hakan ba ta faru ba ranar Laraba, yayin da majalisar ta ɗage zamanta har sai ranar 21 ga watan Disamba, ba tare da duba kasafin ba.
Meyasa majalisa ba ta cigaba da aiki kan kasafin ba?
Shugaban kwamitin majalisa kan kasafin kudi, Jibrin Barau, yace ya zama wajibi su yi haka sabida har yanzun babu kasafin hukumar zaɓe mai zaman kanta, INEC, wanda yake da muhimmanci wajen gudanar da zaɓen 2023.
Rahotanni sun bayyana cewa a halin da ake ciki shugaban INEC, Farfesa Mahmud Yakubu, baya cikin ƙasa, kuma hakan yasa bai kare kasafin kuɗin hukumarsa ba gaban kwamiti.
Farfesa Zuru AbdulRaheen, shine ya wakilci shugaban hukumar zaɓe INEC a gaban kwamitin kasafin kudi domin kare kasafin hukumar ranar Laraba.
Sai dai Farfesa Zuru ya bayyana cewa shugaban INEC ne kaɗai zai iya bayani dalla-dalla kan kuɗaɗen da INEC zata kashe a 2022, kamar yadda Vanguard ta rahoto.
Banda INEC me kuma ya jawo wa kasafin koma baya?
Kazalika rahotanni sun bayyana cewa bayan matsalar rashin kare ƙasafin INEC, majalisar dattawa na jiran hukumar ƙidaya ta ƙasa (NPC) ta zo kare nata kasafin.
A wani labarin na daban kuma Gwamna APC ya shiga shaukin soyayya, ya zuba kalamai masu ratsa zuciya domin taya matarsa murna
Matukar an gina soyayya ta gaskiya kafin aure, to ko mi daren daɗewa wannan soyayyar zata cigaba da karuwa ne ko bayan an zama ɗaya.
Gwamnan Imo, Hope Uzodimma, ya zama misali, inda ya zuba kalamai masu ratsa zuciya domin taya matarsa murnar ƙara shekara.
Asali: Legit.ng