Yan majalisar wakilai sun amince Buhari ya sake karban bashin $5.8bn, ga abubuwa 4 da za'ayi da su

Yan majalisar wakilai sun amince Buhari ya sake karban bashin $5.8bn, ga abubuwa 4 da za'ayi da su

  • Najeriya na shirin sake shiga duniya neman aron makudan kudade don wasu ayyukan jin dadi
  • A ranar Talata majalisar wakilan tarayya tayi zama don amincewa da bukatar shugaba Buhari kan hakan
  • Akwai wasu manyan ayyuka hudu da za'ayi da mafi akasarin kudin idan aka samu nasarar karba

Abuja - Yan majalisar wakilan tarayya sun amincewa Shugaba Buhari ya sake karban bashin kudi Dala biliyan 5.8 da kuma tallafin Dala milyan 10.

Za'a karbi wadannan basussuka ne daga bankin duniya, bankin cigaban Musulunci IDB, Bankin China, Asusun lamunin cigaban Afrika na kasar China, da kuma asusun lamunin cigaban noma.

Yan majalisar sun bukaci a gabatar musu da sharrudan da aka sanyawa Najeriya don bata wadannan basussuka su gani don sanin abin da ya kamata.

Buhari zai sake karban bashin $5.8bn, ga abubuwa 4 da za'ayi da su
Yan majalisar wakilai sun amince Buhari ya sake karban bashin $5.8bn, ga abubuwa 4 da za'ayi da su Hoto: Presidency
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Wahalar da ‘Yan Najeriya suke ciki za ta karu a 2022, Minista ta karo sababbin haraji

Shugaban kwamitin basussuka na majalisa, Ahmed Safana, ya gabatar da jawabin a zauren majalisar, rahoton ChannelsTV.

Safana yace cikin kudin da za'a karba bashi, za'a kashe:

$2.3 billion wajen fadada magudanar wutar lantarki,

$290,000,000 wajen magance zazzabin cizon sauro,

$700,000,000 wajen samar da ruwan sha

$786,382,967 wajen aikin tafkin Gurara, dss.

A cewarsa:

"Majalisa ta amince da wadannan tattaunawa na neman bashi da akeyi a tsarin basussukan 2018-2020."

Asali: Legit.ng

Online view pixel