An gurfanar da wata mata a kotu kan 'cin zarafin' sufetan 'yan sanda a Legas
- An gurfanar da Favour Anueyiagu mai shekaru 32 ranar Laraba gaban kotun majistare da ke Badagry a Legas akan cin zarafin sifetan ‘yan sanda
- Mai gabatar da kara ASP Clement Okuiomose ya sanar da kotu yadda ta aikata laifin a ranar 8 ga watan Disamba da misalin karfe 10:30 a safe kusa da kotun
- A cewar Okuiomose, ta aikata laifin hankada sifeta Modinat Esho har sai da ta fadi kasa yayin da ta ke tsaka da yin aikin da gwamnati ta dauke ta
Jihar Legas - ‘Yan sanda sun gurfanar da wata mata gaban Kotun Majistare da ke Badagry a Jihar Legas bayan cin zarafin sifetan ‘yan sanda, Punch ta ruwaito.
Wacce ake karar ta na fuskantar laifuka biyu ne, daya na cin zarafi sai kuma tayar da zaune tsaye.
Mai gabatar da kara, ASP Clement Okuiomose ya sanar da kotu cewa wacce ake zargin ta aikata laifin ne a ranar 8 ga watan Disamba da misalin karfe 10 na safe a haraban kotun majistaren da ke Badagry a jihar Legas.
Ta ci zarafin sifetan kuma ta tayar da tarzoma
A cewarsa ta ci zarafin sifeta Modinat Esho wacce ma’aikaciya mai lamba 234392 da ke aiki da kotun majistare ta uku a Badagry, ta hanyar hankada ta kasa yayin da ta ke kan aiki.
Okuiomose ya ce wacce ake kara ta tayar da tarzoma ta hanyar hankada mai kara.
Mai gabatar da kara ta ce take a nan aka kama Anueyiagu aka wuce da ita ofishin ‘yan sanda don a dauki mataki akanta.
Ya kara da cewa laifin da ta yi ya ci karo da sashi na 174 da 168 na laifukan jihar Legas na 2015.
Wacce ake zargin ba ta amsa laifinta ba
Duk da dai ta ki amsa laifin da ake zarginta da aikatawa.
Alkalin majistaren, Firdausi Adefioye ta bayar da belin wacce ake karar akan N100,000 sannan ta gabatar da tsayayyu biyu.
Sannan a cewarta, sai tsayayyun sun zama mazauna kusa da kotun kuma su gabatar da shaidar biyan haraji ga gwamnatin jihar Legas.
Ta kuma dage sauraron karar zuwa ranar 12 ga watan Janairun 2022, kamar yadda Punch ta ruwaito.
Kano: Ƴan Sanda Sun Kama Sojan Bogi, Zailani-Ibrahim Da Ya Ƙware Wurin Tatsar Masu Keke Napep
A wani labarin daban, rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta samu nasarar damkar sojan bogi wanda ya kware wurin damfarar masu Napep, The Nation ta ruwaito.
Jami’in hulda da jama’an rundunar, DSP Abdullahi Kiyawa ne ya tabbatar da kamen a wata takarda wacce ya ba manema labarai ranar Talata a Kano.
A cewarsa, wanda ake zargin, Abubakar Zailani-Ibrahim, mai shekaru 27 ya gabatar wa da ‘yan sandan ofishin Rijiyar Zaki kansa a matsayin soja kuma ya je da wani mai Napep.
Asali: Legit.ng