Duniya kenan: Dalibar SSS1 ta zuba guba a abincin uwar rikonta da ta rene ta tun tana karama

Duniya kenan: Dalibar SSS1 ta zuba guba a abincin uwar rikonta da ta rene ta tun tana karama

  • 'Yan sanda sun kame wata yarinya 'yar shekaru 18 da laifin zuba guba a abincin uwar rikonta a jihar Ogun
  • 'Yan sanda sun bayyana cewa, an kama yarinyar ne bayan da uwar rikon ta fahimci an saka mata guba a abinci
  • Yarinyar ta amsa laifin da kanta, inda ta bayyana dalilin da yasa tayi tunanin zuba guba a abincin uwar rikon

Ogun - Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Ogun sun kama wata dalibar makarantar sakandare SSS 1 mai suna Tope Fasanya ‘yar shekara 18 bisa laifin sanya wa uwar rikonta Misis Esther Bada guba.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Abimbola Oyeyemi, ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata 14 ga watan Disamba.

Kara karanta wannan

Farin jinin Shugaba Buhari ya yi mummunan sauka bayan hare-hare da kashe-kashe a Arewa

Dalibar da ta yi yunkurin kashe uwar rikonta
Duniya kenan: Dalibar SSS1 ta zuba guda a abincin uwar rikonta da ta rene ta tun tana karama | Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Oyeyemi ya ce an kama dalibar ne biyo bayan korafin da wacce abin ya shafa ta kai, Daily Trust ta ruwaito.

Ya ce wacce abin ya shafa ta ce ‘yar aikinta ce ta kawo mata abinci, kuma nan da nan bayan ta ci abincin, sai ta ji zafi a cikinta sosai, sai ta ji ba dadi ba kamar yadda ta saba ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce:

“Lokacin da ciwon ya tsananta sai ta kira 'yar aikin ta zo ta ci sauran abincin amma ta ki. Hakan ya sa ta fara zargin wani abu game da 'yar aikin.
“Bayan rahoton, an garzaya da matar da abin ya shafa zuwa babban asibitin Owode-Egba, inda daga nan aka mika ta zuwa cibiyar kula da lafiya ta tarayya da ke Abeokuta domin samun kulawar da ta dace. Daga baya aka kama wacce ake zargin.”

Kara karanta wannan

Duk da Jami’an tsaro, ‘Yan bindiga sun dawo titin Kaduna - Abuja, sun yi barin wuta

Ya ce a lokacin da ake tuhumarta, farko ta musanta zargin, inda aka tura ta zuwa sashin binciken laifuka da leken asiri na jihar.

Oyeyemi, ta ce daga baya, ta amsa da kanta cewa "ta zuba guban bera a cikin abincin wacce abin ya shafa."

Ya ce

“Bincike na farko da aka yi ya nuna cewa wacce ake zargin tana zaune da matar tun tana ‘yar aji uku a firamare, kuma matar ta kasance malamar ajinsu a lokacin.
“Bayan rasuwar mahaifinta, matar ta taimaka wa yarinyar ta hanyar kai ta ba damar ta zauna a gidanta kuma daga nan za ta ke zuwa makaranta da kudinta.
"Wacce aka sanya wa guban ta ce ta dauki nauyin karatun wacce ake zargin har zuwa karatun ta na yanzu."

Ya ce wacce ake zargin ta ce ta yanke shawarar kashe uwar rikon nata ne a yunkurinta na komawa ta gana da mahaifiyarta.

Kara karanta wannan

Matar da tace tana kallo 'yan bindiga suka kona mahaifiyarta da 'ya'ya 4 ta rasu

Oyeyemi ya ruwaito kwamishinan ‘yan sanda, Lanre Bankole, ya bayar da umarnin a gurfanar da yarinyar a gaban kotu da zarar an kammala bincike, kamar yadda The Guardian ta ruwaito.

DSS ta ce jama'a su kula, ana kokarin fara daukar dalibai aikin bindiganci da sace mutane

A wani labarin, hukumar tsaro ta farin kaya (DSS), ta jawo hankalin jama’a kan wani shirin daukar dalibai aikin ‘yan bindiga, garkuwa da mutane, fashi da makami dakuma laifukan satan kudi, kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito.

Kakakin hukumar ta DSS, Dr Peter Afunanya ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai a Abuja ranar Talata 14 ga watan Disamba.

Hukumar ta DSS ta ce baya ga dalibai, ‘yan Majalisar Dokoki/Majalisun Jihohi da ke hutu da sauran ma’aikatan gwamnati da masu zaman kansu da ke hutu na iya fuskantar barazanar tsaro daban-daban.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.