Bayan karbar N8m na fansa, 'yan bindiga sun sheke ma'aikacin lafiya da manajan masana'anta
- Miyagun 'yan bindigan a jihar Niger sun halaka ma'aikacin lafiya tare da manajan gidan ruwan da suka sace bayan karbar kudin fansa har N8 miliyan
- Kamar yadda Kasimu Barangada, wanda ya kai kudin fansar ya bayyana, ya ce sun nuna masa gawar mutum 2 tare da sauran wadanda ba su kashe ba
- A halin yanzu, 'yan bindigar suna bukatar kudi har N20 miliyan da kuma wayoyin salula 2 na fansar gawawwakin da kuma wadanda ke hannunsu
Niger - 'Yan bindiga sun halaka wani ma'aikacin lafiya da kuma manajan gidan ruwa da aka sace a garin Tegina da ke karamar hukumar Rafi ta jihar Niger bayan karbar kudin fansa har naira miliyan takwas.
'Yan bindigan sun bukaci kudin fansar gawar da sauran mutanen da ke hannunsu har naira miliyan ashirin kuma sun bukaci a kawo musu wayar salula.
Ma'aikacin lafiyan mai suna Sani Garba, mazaunin garin Tegina ne kuma shi ke kula da fannin riga-kafi a karamar hukumar Rafi ta jihar.
Ya na daga cikin wadanda aka sace a garin Tegina a ranar 14 ga watan Nuwamba a wani gidan ruwa. Manajan gidan ruwan mai suna Kasimu Lawan duk 'yan bindigan sun hada sun kashe su.
Premium Times ta ruwaito cewa, an sace su ne a Tegina, garin da aka sace daliban Islamiyya 136 a watan Mayun shekarar nan.
An sako dalibai casa'in daga cikin daliban islamiyyan a watan Augusta bayan iyayen sun hada kudi har naira miliyan sittin tare da siyan babura biyar a matsayin kudin fansa.
Makonni kafin aukuwar lamarin, 'yan bindigan sun sace dalibai daga wata makarantar gwamnati da ke Kagara a yankin.
A ranar Talata, jami'in hukumar sufuri ta garin, Bello Muhammad, ya sanar da Premium Times cewa an hada kudi har miliyan takwas domin biyan kudin fansar wadanda aka sace.
Sai dai kuma, bayan biya, an sanar da jama'a cewa 'yan bindigan sun kashe mutum biyu daga cikin wadanda aka sace.
Muhammad ya ce wani daga cikin wadanda aka sace, Mas'udu Ibrahim, ya tsero daga hannun maharan yayin da Bako BK, mamallakin gidan ruwan duk suna hannun 'yan bindigan
Muhammad ya ce wanda ya kai kudin fansar ya dawo da mugun hoton mamatan wanda hakan yasa aka yi musu Salatul Ghaib.
'Yan bindigan a halin yanzu suna bukatar miliyan ashirin, babura uku da wayoyin shafawa biyu a matsayin kudin fansar gawawwakin da kuma wadanda ke hannun su, Muhammad yace.
Wanda ya kai kudin fansar mai suna Kasimu Barangada, ya bayar da labarin yadda ya kai kudin fansar har dajin a ranar Talata da ta gabata.
Da Dumi-Dumi: ’Yan Bindiga Sun Afka Etekwuru, Sun Kashe Mutum 2 Sun Lalata Dukiyoyin Miliyoyin Naira
Ya ce masu garkuwa da mutanen sun rufe masa ido yayin da suka shiga da shi daji. Ya ce gawar mamatan na kwance a kasa yayin da BK ba ya iya ko magana.
Jihar Niger: 'Yan bindiga na karbar sigari da wiwi a matsayin kudin fansa
A wani labari na daban, 'yan bindiga da suka addabi yankunan karamar hukumar Munya ta jihar Niger suna tirsasa mazauna yankin wurin ba su fakitin sigari da sunkin wiwi domin fansar 'yan uwansu da suka sata.
Daily Trust ta ruwaito cewa, jama'a masu tarin yawa na yankunan Zazzaga, Cibani da sauransu da ke karamar hukumar Munya suna hannun masu garkuwa da mutane.
Wani mamba na kwamitin tsaro a yankin ya sanar da cewa, sun kai wadannan kayayyakin ga 'yan daban a ranar Talata kafin su sako wasu daga cikin wadanda aka sace.
Asali: Legit.ng