Da Dumi-Dumi: Shugaba Buhari ya gabatar da sabon ministan Lantarki ga Majalisa

Da Dumi-Dumi: Shugaba Buhari ya gabatar da sabon ministan Lantarki ga Majalisa

  • Tun bayan da shugaba Buhari ya sallami ministan lantarki, Sale Mamman, bai maye gurbinsa ba
  • Buhari ya tura da sunan Muazu Sambo, daga jihar Taraba ga majalisa domin tantace shi a matsayin sabon ministan lantarki
  • Shugaban ya kuma aike da sunayen kwamishinonin hukumar zaɓe INEC, da na hukumar kidaya NPC, domin tantancewa

Abuja - Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya gabatar da sunan Muazu Sambo, a matsayin sabon ministan da zai naɗa daga jihar Taraba ga majalisar dattijai.

Dailytrust ta ruwaito cewa Sambo zai maye gurbin tsohon ministan lantarki, Sale Mamman, wanda shugaban ya sallama daga aiki tare da tsohon ministan noma, Sabo Nanono a watan Satumba da ya gabata.

Shugaban majalisar dattijai, Sanata Ahmad Lawan, shine ya karanta wasikar neman amincewa da shugaba Buhari ya aike wa majalisar a zamanta na yau Talata.

Kara karanta wannan

Babbar magana: EFCC ta maka Fami Fani-Kayode a kotu bisa wasu laifuka 12

Shuagba Buhari
Da Dumi-Dumi: Shugaba Buhari ya gabatar da sabon ministan Lantarki ga Majalisa Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

Buhari ya naɗa kwamishinonin INEC

Haka nan kuma, shugaba Buhari ya bukaci majalisar ta tantance sabbin kwamishinonin zaɓe na ƙasa da kwamishinan zaɓen jiha guda ɗaya na INEC.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Waɗan da shugaban ya nemi majalisa ta amince da su sun haɗa da; kwamishinonin zaɓe, Malam Mohammed Haruna (Niger), May Agbamuche Mbu (Delta), Okeagu Kenneth Nnamdi (Abia) da Manjo Janar A.B. Alkali (mai ritaya.) (Adamawa).

Sauran sun haɗa da; Farfesa Rada H. Gumus (Bayelsa), Sam Olumeko (Ondo) duk a matsayin kwamishinonin INEC na ƙasa, sai kuma Olaniyi Olaleye Ijalaye (Ondo) a matsayin REC.

Wasu daga cikin kwamishinonin hukumar zabe INEC sun yi aiki tare da shugaban INEC, Farfesa Mahmud Yakubu, a zangon mulkinsa na farko, wanda daga baya Buhari ya sake naɗa shi a karo na biyu.

Buhari ya naɗa kwamishinonin NPC

Kazalika shugaban ƙasa Buhari ya nemi amincewar majalisar dattawan wajen naɗa kwamishinonin hukumar kidaya ta ƙasa (NPC).

Kara karanta wannan

Kungiyar IZALA ta bada umarnin fara Alkunut a masallatan Ahlissunnah dake fadin Najeriya

Waɗanda shugaban ya aike da sunayen su sun haɗa da; Injiniya Benedict Opong (Akwa Ibom), Gloria Izofor Mni, Barista Patricia O. Iyayan Kuchi (Benue), Dakta Bala Haliru (Kebbi) da kuma Dakta Iyatayo Oyetunbi (Oyo).

A wani labarin kuma hadimar Buhari ta bayyana yadda Manjo Hamza Al-Mustapha ya terad da ita daga yi mata fyaɗe

Shugaban hukumar yan Najeriya dake kasashen waje (NIDCOM), Abike Dabiri-Erewa, ta bayyana irin kalubalen da ta shiga ta yadda aka kusa mata fyaɗe lokacin da take aikin jarida.

Tsohuwar yar majalisar tarayya ta shaidawa yan jarida su tashi tsaye kuma su ƙarfafa kansu, su rinka gudanar da binciken kwakkwafi kan wani abu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262