Da dumi-dumi: Gwamna ya kori kwamishinan lafiya saboda yi masa katsalandan
- Gwamnan jihar Ribas ya kori wani kwamishinansa bayan da ya gano ya shirya taro ba tare da izinin gwamnan ba
- Ya kori kwamishinan ne a gaban wasu likitocin da suka kawo masa ziyara a fadar gwamnati tare da bayyana dalilai
- A halin da ake ciki, gwamnan ya gana da likitocin, inda ya yi alkawarin kawo ci gaba a harkokin kiwon lafiyar jihar
Ribas - Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya kori kwamishinansa na ma'aikatar lafiya, Farfesa Princewill Chike, Channels Tv ta ruwaito.
Gwamna Wike ya bayyana hakan ne a zauren majalisar zartarwa ta Jiha a ranar Litinin yayin wata ziyarar ban girma da jami’an kungiyar likitoci ta Najeriya suka je gidan gwamnati domin yi masa bayani kan taron kasa da suka gudanar a Fatakwal.
Gwamnan ya fusata cewa korarren kwamishinan ya amince da gudanar da taron kawai ba tare da bin ka’ida ba.
Ya ce ya samu labarin taron ne ta hanyar sakon waya da kwamishinan ya aika masa inda yake neman a samar da kayan aiki ba tare da wani bayani na sirri ba ko kuma a lokacin taron majalisar zartarwa ba.
A cewarsa, rashin tsarin da Farfesa Chike ya nuna ya kawo cikas ga gwamnatinsa, cewa ziyarar ban girma da hukumar lafiya ta kawo masa ta yi daidai da ranar da majalisar zartarwa ta jihar ta amince da ci gaba da kaddamar da ayyuka.
Don haka gwamnan ya bukaci kwamishinan da ya fita a taron kafin ya gana da ma’aikatan kungiyar lilitocin lafiya da na hakora, inda ya yi alkawarin kara inganta harkokin kiwon lafiya a jihar Ribas.
SaharaReporters ta ruwaito gwamnan yana cewa:
“A gaskiya ban taba ganin abin kunya irin wannan ba a rayuwata. Kowa ya san cewa da dabi'a ta bace kawo mutane kuma ba za a iya halartan su ko harbar bakuncinsu ba. Don haka duk wanda ya yi haka zai yi kuka da kansa.”
Babbar magana: Wata mata ta rasa aikinta saboda tsananin yin 'Bleaching'
A wani labarin, wata 'yar Najeriya mai suna Ikot Sharon ta ba da labarin yadda wani gidan cin abinci ya bai wa wata ma’aikaciya takardar kora saboda bilicin da rashin daidaito a launin fatarta.
Da take ba da labarin dalilin da yasa aka kori matar a shafin Twitter, @IkotSharon ta ce fatar ma'aikaciyar ya yi muni wanda ya haifar da duhun kullin hannayenta wanda ya bambanta da farar fatarta.
Wani bangare na rubutun Twitter din yana cewa:
"Haka wata mata aka koreta yau saboda tayi bilicin sosai, kullin hannayenta sunyi duhu yayin da jikinta yayi fari."
Asali: Legit.ng