Jami'an tsaro sun kai farmaki sun kamo 'yan bindiga 30, sun ceto wani sarki da aka sace

Jami'an tsaro sun kai farmaki sun kamo 'yan bindiga 30, sun ceto wani sarki da aka sace

  • Wani samame na hadin gwiwa da jami'an tsaro suka yi ya kai ga nasarar cafke wasu mutane 30 da ake zargin masu garkuwa da mutane ne a jihar Imo
  • Wannan farmakin ya zo ne sa’o’i 48 bayan wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba suka sace wasu manyan sarakunan gargajiya biyu a jihar
  • A yayin farmakin an ceto daya daga cikin sarakunan, yayin da gwamnatin jihar ke ci gaba da baiwa mazauna jihar tabbacin tsaron lafiyarsu

Imo - An kama wasu mutane 30 da ake zargin masu garkuwa da mutane ne da ke aikata laifuka a jihar Imo, kamar yadda gidan talabijin na Channels ya ruwaito.

An kama barayin ne a wani samame da rundunar hadin guiwa ta jami’an tsaro suka kai a sansanoninsu da ke yankunan Orsu da Uli a karamar hukumar Ihiala ta jihar Anambra.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Yan ta'addan ISWAP sun gwabza da Mafarauta a Jihar Borno

Taswirar jihar Imo
Yanzu-Yanzu: Jami'an tsaro sun kamo 'yan bindiga 30, sun ceto wani sarki da aka sace | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Wani basaraken gargajiya da aka yi garkuwa da shi a karamar hukumar Okigwe ranar Lahadi, Acho Ndukwe na yankin Ihube mai cin gashin kansa, shi ma an ceto shi a yayin farmakin.

Wannan samame dai na zuwa ne mako guda bayan da hukumar tsaro ta farin kaya ta Najeriya NSCDC ta kwato bindigogi kirar kasashen waje guda 33, masu sarrafa kansu da kayan aikin tsaftace bindigu guda 15 daga wata maboyar ‘yan ta’adda a jihar Imo.

Kwamandan NSCDC a Imo, Michael Ogar, ne ya bayyana haka yayin da yake zantawa da manema labarai a Owerri a ranar Alhamis, 9 ga watan Disamba.

Ogar ya jera abubuwan da aka kama wadanda suka hada da; Bindigogi guda 26, bindigogin harbi ka labe guda biyu, da kuma kayan aikin tsaftace bindiga guda 15.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: An Kashe Fitaccen 'Dan Kasuwan Najeriya a Afirka ta Kudu

Kwamandan ya ce jami’an sa da suke aiki da sahihan bayanan da suka samu kan inda masu laifin suke, sun yi kwanton bauna na ‘yan kwanaki kafin su mamaye maboyar tare da kwato kayayyakin.

'Yan bindiga sun yi awon gaba da sarakuna biyu, sun kone fada

Da safiyar jiya Lahadi, wasu tsagerun yan bindiga suka kaddamar da mummunan hari kan kauyukan jihar Imo,.inda suka sace sarakuna biyu.

Jaridar Punch ta rahoto cewa maharan sun kone fadar sarakunan da suka sace, sannan suka kone motocinsu yayin harin.

Sarakunan gargajiyan da lamarin ya shafa sune; Acho Ndukwe na Amagu Ihube da kuma Paul Ogbu na yankin Ihitte Ihube, duk a karamar hukumar Okigwe, jihar Imo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.