Da Duminsa: Yan bindiga sun yi awon gaba da sarakuna biyu, sun ƙone fada
- Wasu yan bindiga sun farmaki kauyukan jihar Imo, inda suka yi awon gaba da sarakunan gargajiya guda biyu
- Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun ƙone fadar sarakunan da suka sace da motocin su na hawa
- Hukumar yan sandan jihar ta bayyana cewa a halin yanzu jami'anta na kan gudanar da bincike kan lamarin
Imo - Da safiyar yau Lahadi, wasu tsagerun yan bindiga suka kaddamar da mummunan hari kan kauyukan jihar Imo,.inda suka sace sarakuna biyu.
Jaridar Punch ta rahoto cewa maharan sun kone fadar sarakunan da suka sace, sannan suka kone motocinsu yayin harin.
Sarakunan gargajiyan da lamarin ya shafa sune; Acho Ndukwe na Amagu Ihube da kuma Paul Ogbu na yankin Ihitte Ihube, duk a karamar hukumar Okigwe, jihar Imo.
Yan bindigan kuma sun sace shugaban matasa na Umulolo Okigwe, wanda har yanzun ba'a gano ainihin sunansa ba.
Yadda lamarin ya faru
Wata majiya daga yankin da lamarin ya faru, ya shaida wa manema labarai cewa harin ya kwashi tsawon awa ɗaya daga 12:00 na dare zuwa karfe 1:00.
Vanguard ta rahoto Mutumin yace:
"Wani abu ne daban ya faru da safiyar Lahadi, sun zo a cikin motar Hilux kuma suka sace sarakuna biyu, suka kona fadarsu da motocin su."
"Daga nan kuma suka je gidan Fabian Nwosu, suka kona gidansa yayin da suka ga yana nan. Eze Ndukwe basarake ne mai ƙima, shine shugaban kungiyar sarakunan karamar hukumar Okigwe."
"Babu wanda ya fahimci wannan harin, baki ɗaya, yankin ya shiga yanayin ruɗani da tashin hankali."
Wane mataki yan sanda suka ɗauka?
Kakakin rundunar yan sanda reshen jihar Imo, Micheal Abattam, ya bayyana cewa hukumar su ta fara gudanar da bincike kan lamarin.
A wani labarin kuma matar kwamishinan kimiyya da fasaha a Katsina, wanda aka kashe a gidansa ta yi magana
A ranar Laraba da ta gabata ne wasu mutane suka je har gida suka kashe kwamishinan kimiyya da fahata na jihar Katsina.
Matar marigayi Dakta Rabe Nasir, ta bayyana irin kulawar mijinta da soyayyarsa kuma tace a jami'a suka haɗu da shi.
Asali: Legit.ng