Sheikh Gumi: 'Yan bindiga sun sace yayana, sun kashe dan direban gidanmu

Sheikh Gumi: 'Yan bindiga sun sace yayana, sun kashe dan direban gidanmu

  • Sheikh Gumi ya yi fatali da kakkausar murya kan batun cewa yana tallafawa da daukar nauyin ‘yan bindiga da ke addabar arewa
  • Malamin mazaunin Kaduna ya ce shi ma ya shaida matsalar ‘yan ta’addan, inda ya kara da cewa zargin da ake masa ba gaskiya bane
  • Gumi ya ce ‘yan bindigan sun yi garkuwa da yayansa, sannan kuma sun kashe dan gidansu wani direban mota

Kaduna - Shahararren malamin addinin Islama, Sheikh Ahmad Gumi ya bayyana cewa shi ma ya sha fama da hare-haren ‘yan bindiga da ke addabar arewa.

Ya ce an yi garkuwa da yayansa kuma sai da ya biya kudin fansa domin a sake shi.

Malamin na Kaduna ya bayyana hakan ne a wata hira da jaridar Premium Times ta wallafa a ranar Lahadi, 12 ga watan Disamba.

Kara karanta wannan

Bayan barranta da 'yan bindiga, Gumi ya tura sako ga masu cewa ya kamata a kama shi

Sheikh Gumi da 'yan bindiga
Sheikh Gumi: 'Yan bindiga sun sace yayana, sun kashe dan direban gidanmu | Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Gumi ya bayyana haka ne a lokacin da yake mayar da martani kan zargin da ake masa na daukar nauyin ‘yan bindiga da kuma tallafa musu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Malamin da ake cece-kuce akansa ya sha neman gwamnatin tarayya da ta yi wa ‘yan bindiga afuwa, ya ce ba daidai bane a ce yana goyon baya ko daukar nauyin miyagu.

Yace:

"Ni ma lamarin 'yan bindiga ya shafe ni."
Da aka tambaye shi ko ta wacce hanya hakan ya shafe shi, malamin ya budi baki ya ce:
“An yi garkuwa da yayana, sai da muka biya kudin fansa, haka nan a masallacin mu mun biya kudin fansa, ko a yanzu wani yana neman na taimaka masa ya biya kudin fansa.
“Yan bindiga ne suka kashe dan direban gidanmu wanda ya kasance dan uwanmu, dan soja ne , to ta yaya zan iya tallafawa irin wadannan mutane?"

Kara karanta wannan

Kabiru Alhasan: Mai hannu daya mai yin sana'ar faskaren itace domin ya rayu a Duniya

Ta yaya za a magance matsalolin 'yan bindiga?

Da aka tambaye shi ta yaya Najeriya za ta iya magance matsalar ‘yan bindiga baya ga yi musu afuwa, Gumi ya ce:

“Magance su na da matukar muhimmanci domin kaso mai yawa na masu daukar makamai suna barna ne saboda wasu dalilai, ba wai don kudi kawai ba.

Malamin ya kara da cewa:

"Akwai batun kabilanci a cikin a lamarin, yanzu kuma batun addini na kokarin kutsawa ciki ko kuma ya riga ya kutsa, lamarin da ya kara ta'azzara batun."

Ya ce yin amfani da sojoji wajen magance ‘yan bindigar “kamar kashe kuda ne da guduma.”

Bayan barranta da 'yan bindiga, Gumi ya tura sako ga masu cewa ya kamata a kama shi

A tun farko, shahararren malamin addinin musuluncin nan, Sheikh Ahmad Gumi, ya bayyana masu kira da a kamo shi kan alaka da ‘yan bindiga da ke addabar yankin Arewacin Najeriya a matsayin wawaye.

Kara karanta wannan

Bayan shekaru 2 ana wahala, Bill Gates ya fara hango karshen annobar annobar COVID-19

Gumi dai duk da bacin ran da jama’a suke nunawa, ya sha ganawa da wasu ‘yan bindiga inda ya bukaci gwamnatin tarayya da ta yi musu afuwa kamar yadda ta yi wa tsagerun Neja Delta.

Sai dai ‘yan Najeriya da dama sun yi kira da a damke malamin da ke zaune a Kaduna, inda suka zarge shi da daukar nauyin ‘yan bindigar da kuma tallafa musu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.