Yadda wani gwamna a Arewa ya kwashi tsabar kudi biliyan N60bn daga lalitar jiharsa, EFCC ta magantu
- Hukumar EFCC tace sabon sashin da ta kirkiro na fasaha ya fara aiki, domin zuwa yanzun ya gano wasu bayanan sirri
- Hukumar tace ɗaya daga cikin abubuwan da sashin ya bankado shine yadda wani gwamna ya cire kudi daga lalitar jiharsa
- Bawa yace hukumarsa na cigaba da aiki kafaɗa da kafaɗa da wasu hukumomi domin inganta aikin
Abuja - Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa (EFCC) ta maka alama kan wani gwamnan Arewa bisa zargin ya kwashi tsabar kudi biliyan N60bn daga lalitar gwamnatin jiharsa.
Hukumar ta bayyana haka ne a wani sabon bayani da ta fitar yau, Lahadi 12 ga watan Disamba, 2021, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
Sai dai EFCC tace gwamnan ya fito ne daga arewa maso tsakiya a Najeriya amma ba ta faɗi ainihin sunan shi ba, kamar yadda Tribune ta rahoto.
Shugaban EFCC, Abdulrasheed Bawa, shine ya bayyana haka a wurin taron mujallar hukumar, "EFCC Alert."
Dailytrust ta rahoto Bawa yace:
"Wani gwamna daga cikin gwamnonin jihohin arewa ta tsakiya cikin shekaru shida da suka shuɗe (mutum ɗaya) ya zare tsabar kudi biliyan N60bn."
"Ba wai muna son mutane su yi ta yama ɗiɗi da mu a shafukan jaridu ko a taron manema labarai bane, muna aiki ne ta bayan fage domin fatattakar cin hanci, kuma ba da jimawa ba yan Najeriya zasu ga abinda muke yi."
"Ina mai shaida muku sabon sashin da muka kirkira na fasaha ya fara baiwa mara ɗa kunya. Sun gano wasu bayanan sirri da dama. Ɗaya daga cikin shine batun wannan gwamnan daga arewa ta tsakiya."
Gwamnonin arewa ta tsakiya da suka kai shekara 6 kan mulki
Jihohi guda shida da Najeriya ke da su a yankin arewa ta tsakiya sune; Kwara, Benuwai, Neja, Nasarawa, Filato da Kogi
Daga cikin waɗan nan jihohi, gwamnan Filato, Simon Lalong, gwamnan Benuwai, Samuel Ortom, gwamnan Neja Abubakar Sani Bello, da gwamnan Kogi, Yahaya Bello, sune suka shafe shekara 6 a kan mulki.
Shin dagaske EFCC ta rufe kundin tsofaffin gwamnoni?
Bawa ya kuma musanta zargin da ake jingina wa EFCC cewa ta rufe kundin tuhumar da take wa tsofaffin gwamnoni ta jefa karkashin kafet.
Yace hukumar da yake jagoranta tana bin komai a hankali ne amma ba kamar yadda wasu ke tunani ba.
"Ina tabbatar muku da cewa muna kan aiki, bamu cika son magana kan abinda ke karkashin bincike ba. Dagaske ne mun gayyaci tsohon gwamna Lucky Igbinedion don amsa wasu tambayoyi."
"Yana tare da mu na tsawon kwana biyu, kuma mun sallame shi. A halin yanzu muna cigaba da bincike tare da kula wa, kada mu jefa kan mu cikin wata matsala."
A wani labarin na daban kuma matar kwamishinan kimiyya da fasaha a Katsina, wanda aka kashe a gidansa ta yi magana
A ranar Laraba da ta gabata ne wasu mutane suka je har gida suka kashe kwamishinan kimiyya da fahata na jihar Katsina.
Matar marigayi Dakta Rabe Nasir, ta bayyana irin kulawar mijinta da soyayyarsa kuma tace a jami'a suka haɗu da shi.
Asali: Legit.ng