'A jami'ar BUK na fara haɗuwa da shi', Matar kwamishinan da aka kashe a Katsina ta magantu
- A ranar Laraba da ta gabata ne wasu mutane suka je har gida suka kashe kwamishinan kimiyya da fasaha na jihar Katsina
- Matar marigayi Dakta Rabe Nasir, ta bayyana irin kulawar mijinta da soyayyarsa kuma tace a jami'a suka haɗu da shi
- Yayan mariyagin sun bayyana yadda mahifinsu yake da kuma halin da suka shiga na kashe shi
Katsina - Gaskiya, riko da addini, biyayya, kirki, sanin ya kamata, maida hankali kan aiki, da kuma rashin lamurtan cin hanci na daga cikin kalaman da mahaifiya, mata da yayan Dakta Rabe Nasir suka siffanta shi.
Dailytrust ta rahoto cewa dakta Nasir shine kwamishinan kimiyya da fasaha da aka kashe a gidansa dake cikin garin Katsina.
Kisan kwamishinan ya tada wa mutane da hankali musamman iyalansa da abokan aikinsa, waɗanda suka san cewa shi wani mutum ne da bashi da matsala da kowa, kamar yadda The Cable ta ruwaito.
Mutum ne mai kula da iyalansa - Matar marigayin
Ɗaya daga cikin matansa, Hajiya Binta, ta bayyana cewa ta kasance tare da mijinta na tsawon shekara 38.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A jawabinta, Binta tace:
"Mun haɗu da shi a jami'ai BUK Kano, lokacin muna ɗalibai. Ya bani aji ɗaya, kuma yana karatun kimiyyar siyasa ni kuma ina karanta Tarihi a lokacin. Mun haɗu da shi a wurin zaɓen kungiya, muka gina soyayya da ta kai ga aure shekarar da na kammala karatu.
"Mutum ne mai gaskiya da kirki, yana kula da iyalansa. Mun haifi yara 10 da shi, guda 4 ne suka rayu. Yana kula da addininsa sosai, duk abinda ya shafi addini yana ɗaukarsa da muhimmanci musamman salloli 5 na kowace rana."
"Maganar da muka yi ta ƙarshe da shi, shine lokacin dana nemi izinin zuwa Kano ɗaura auren kanwata, ya mun fatan sauka lafiya. A ranar da aka kashe shi ya turamun hotuna a Whatsapp. Tabbas zamuyi kewarsa."
Uba ne da ba zamu samu kamarsa ba - Ƴaƴan marigayi
Ɗiyarsa, Hafsat Rabe tace:
"Mahaifinmu uba ne da samun kamar shi zai wahala, ba zamu taɓa samun wanda zai maye gurbinsa ba. Ya nuna mana soyayya da kulawa, zai taimaka maka kuma ya baka shawara."
"Maganar karshe da muka yi da shi, shine lokacin da yaje Abuja, kafin ya dawo Katsina. Ya kawo mun ziyara har gidan mijina, shine karo na karshe dana ganshi."
Hakanan kuma wata ɗiyarsa, Nafisa Nasir, wacce lauya ce, tace:
"Mutum ne da ke son kowa da alheri, baya kaunar rikici, irin kisan da aka masa abun takaici ne matuka kuma alama ce dake tabbatar da babu tsaro a kasar nan."
"Mutumin kirki ne na ƙarshe amma irin mutuwar da ya yi ba ta yi kyau ba sam, ta yadda ko makiyin ka ba zaka so ya shiga irin yanayin ba."
"Zamu tabbatar da mun cigaba daga irin tubalin da ya gina mu a kai wanda ya kasance mai kyau, zama mutanen kirki kuma masu kwarin guiwa."
Babban ɗansa, Salim Nasir, ya bayyana mahaifinsa a matsayin uba mai kula da yayansa kuma mutum nagari da samunsu yake wahala.
"A wurina babu kamarsa wajen gaskiya, kirki ga mutane kuma ya tabbatar a matsayina na babban ɗansa, wanda nake da yan uwa mafi yawa mata, na maida hamkali wajen haɗin kan ƴaƴansa, kuma zan ɗora daga nan Insha Allah."
A wani labarin kuma Gwamnatin Masari ta buɗe layukan sadarwa da aka datse a wasu yankunan jihar Katsina
Gwamnatin jihar Katsina karkashin jagorancin gwamna Aminu Bello Masari, ta sanar da dawo da amfani da layukan sadarwa a sassan jihar.
Rahoton Aminiya Hausa ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta dawo da sabis da ta datse a baya a yunkurin dakile yawaitar ayyukan yan bindiga a wasu yankunan jihar.
Asali: Legit.ng