Jigon APC ya bayyana sirri, ya zayyano yadda Atiku ya nemi sadakan kudi daga Tinubu

Jigon APC ya bayyana sirri, ya zayyano yadda Atiku ya nemi sadakan kudi daga Tinubu

  • Tsohon shugaban jam’iyyar APC, Bisi Akande, ya ci gaba da tofa albarkacin bakinsa kan wasu batutuwa tsakanin Tinubu da wasu ‘yan siyasa
  • A cewar Akande, tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar a ko da yaushe yana neman goyon bayan shugaban jam’iyyar APC Tinubu
  • Wadannan bayanan na kunshe ne a cikin littafin tarihin rayuwar Akande mai suna “My Participations” wanda aka kaddamar a Legas a ranar Alhamis, 9 ga watan Disamba

Kamar yadda Cif Bisi Akande, tsohon shugaban APC, ya yi ikirarin cewa tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya nemi kudi daga hannun Bola Tinubu, shugaban APC na yanzu a lokacin da ya dauki fito takara a shekarar 2007.

Ya bayyana hakan ne a cikin littafin tarihin rayuwarsa mai suna “My Participations” wanda aka kaddamar a Legas ranar Alhamis, inji rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Farfesa Jega ya fallasa dabarun Alkalai, ya bayyana yadda suke samun kudin haram

Tsohon shugaban jam'iyyar APC, Cif Bisi Akande
Jigon APC ya bayyana sirri, ya zayyano yadda Atiku ya nemi sadakan kudi daga Tinubu | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

A yakin neman zabe da Obasanjo a shekarar 2007, Atiku ya fice daga PDP inda ya samu tikitin takarar shugaban kasa a jam'iyyar AC.

A cikin littafin My Participations”, Akande wanda kuma shi ne shugaban jam'iyyar AC na kasa a lokacin, ya ba da labarin wasu abubuwan da suka faru a bayan fage a zaben 2007.

A cewarsa:

“A shekarar 2007 mun kafa jam’iyyar AC tare da Abubakar Atiku. Mun amince Atiku ya zama dan takararmu na shugaban kasa kuma mun fahimci cewa zai yi takara tare da Bola Tinubu.
"Ni ne shugaban AC. Wata rana bayan mun tsayar da Atiku a matsayin dan takarar shugaban kasa, sai wani matashi ya zo ya ba ni fom na INEC.
"Na ce masa ba zan iya sanya hannu a kan takardar ba, kuma ni a matsayina na shugaban jam'iyya, dole ne in san sunan da za a cike a ciki.

Kara karanta wannan

Akande: Tsohon Shugaba Obasanjo ya karya kowa, Tinubu kadai ya gagare sa a 2003 – Buhari

“Mun yi imanin Atiku ya kamata ya zabi abokin takararsa daga AD ko da kuwa ba ya son Tinubu.
"Da Atiku, jam’iyyar za ta yi karfi a Arewa, amma saboda rinjayen PDP a Kudu maso Gabas da Kudu-maso-Kudu, za ta kara fuskantar turjiya a yankin.
"Obasanjo ya sauka daga karagar shugaban kasa. Don haka Yarbawa hatta ‘yan tsirarun da suka ci moriyar mulkinsa na girman kai, ba za su kara kada wa PDP kuri’a ba.
“Tun da farko Segun Osoba, Niyi Adebayo da Lam Adesina sun gana da Atiku, muka kawo masa zabin Tinubu, kuma ya yi alkawarin zai dawo mana. Ya ba mu kwanan wata. A wannan ranar, dukanmu muka taru. Atiku ya zo da Audu Ogbe, Tom Ikimi da Usman Bugaje.
“Mun ba da shawarar cewa Tinubu ya zama abokin takararsa, duk da cewa Tinubu ba ya wurin taron. Atiku bai ba mu amsa cikin gaggawa ba. Yace yana son a kara yin shawari.

Kara karanta wannan

An ba Bola Tinubu shawarar ya hakura da neman takarar Shugaban kasa a zaben 2023

“Ikimi, Ogbe da sauran su duk sun yi tasiri sosai a kan Tinubu, domin sun ce hakan na nufin tikitin duk musulmai ne. Mun kashe batun a kan haka. Atiku bai taba cewa komai ba. Muka bar taron.
"Abin da ya tunzura mu shi ne, duk lokacin da muka ce muna bukatar kudi, Atiku zai ce ‘Bola, don Allah a taimake mu’. Bola ne kadai ke kashe kudi a tsakaninmu. Sauran mu talakawa ne.
"Tinubu ya kuma yi amfani da karfinsa da dukiyarsa wajen kafa AC kuma mun ga ya cancanci a ba shi tikitin takara. Mun tattauna da Bola akan haka, ya ce mu tattauna da Atiku.
"Bayan mun kashe batun ne suka kawo min fom din da ba a cike ba. Don haka Atiku ya yi takara da Obi ya fadi. Jihar Legas ce kadai daga Kudu maso Yamma suka zabi Atiku a dukkan jihohin Najeriya.”

Bisi Akande mai gaskiya ne, bai taba amsa ko bayar da cin hanci ba, inji Buhari

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: Kotu ta tsige shugaban jam'iyyar APC na tsagin Ministan Buhari

A wani labarin, shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana Cif Bisi Akande, tsohon shugaban riko na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a matsayin ma'aikacin gwamnati mai gaskiya da rikon amana, Daily Trust ta ruwaito.

Buhari, wanda shine babban bako na musamman wurin gabatar da littafi da Bisi Akande ya rubuta kan rayuwarsa ya ce marubucin bai taba sauya halinsa ba tun yana aikin gwamnati da bayan ya gama, na rashin karba ko bada rashawa.

Ya karanto daga shafi na 400 a cikin littafin inda Akande ya rubuta cewa bai taba nema ko bada cin hanci ba a rayuwarsa, ya kuma jadada cewa kamilin mutum ne mai gaskiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.