Kano: Bayan Amsa Gayyatar SSS, Ɗaya Cikin Wadanda Suka Shirya Zanga-Zanga Ta Ce Ta Tsamme Hannunta

Kano: Bayan Amsa Gayyatar SSS, Ɗaya Cikin Wadanda Suka Shirya Zanga-Zanga Ta Ce Ta Tsamme Hannunta

  • Zainab Naseer Ahmed, daga daga cikin wadanda suka shirya zanga-zangar lumana na janyo hankalin gwamnatin kan halin rashin tsaro a Arewa ta ce tsamme hannunta daga cigaba da zanga-zangar
  • Zainab ta bayyana hakan ne cikin wata wallafa da ta yi a shafinta na Facebook jim kadan bayan ta fito daga ofishin SSS bayan sun gayyace ta, ta shawarci sauran masu zanga-zangar su yi zamansu a gida
  • A cewarta, ta samu bayyanai da ke nuna wasu na son amfani da zanga-zangar domin cimma wata buri na siyasa don haka tana fargabar akwai yiwuwar jefa masu zanga-zangar cikin hatsari

Kano - Daya daga cikin wadanda suka shirya zanga-zangar #NoMoreBloodshed a Kano, Zainab Naseer Ahmed, ta ce ta tsame hannun ta daga zanga-zangar, jim kadan bayan fitowa daga ofishin yan sandan farin kaya, SSS.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: SSS ta gayyaci daya daga cikin wadanda suka shirya zanga-zanga a Arewa

Tunda farko SSS ta gayyaci Zainab ne domin amsa tambayoyi kan rawar da ta taka wurin shirya zanga-zangar da aka yi a wasu jihohin arewa da Abuja don janyo hankalin gwamnati kan rashin tsaro a arewa bayan kisar gillar da aka yi wa matafiya 42 a Sokoto.

Bayan shafe kimanin awa biyu a ofishin SSS, Zainab Ahmad ta wallafa a shafinta na Facebook cewa daga yanzu ta tsame hannun ta daga zanga-zangar.

Mi'ara koma baya: Bayan amsa gayyatar SSS, wacce ta shirya zanga-zanga a Kano ta ce ta janye
Bayan amsa gayyatar SSS, Zainab Naseer Ahmed ta tsame hannunta daga zanga-zangar Kano. Hoto: Zainab Naseer Ahmed
Asali: Facebook

Ta kuma yi kira ga sauran masu zanga-zangar da cewa su kauracewa cigaba da zanga-zangar su yi zamansu a gidajensu.

Kalamanta:

"Ina son in sanar da mutane cewa daga yau, na tsamme hannu na daga zanga-zangar da aka fara a yau. Ina shawartar mutane na a Kano su kauracewa zanga-zangar na gobe.

Kara karanta wannan

Matasa Sun Fita Gari Sunyi Zanga-Zanga Kan Yawaitar Kashe-Kashe a Arewa

"An sanar da ni wasu abubuwa, kuma na damu da lafiyar mutane bana son wani abu ya same su sakamakon zanga-zangan. Yin zanga-zanga gobe a Kano yana da hatsari domin na samu bayanin wasu na son amfani da zanga-zangar don cimma manufar siyasa.
"Ina bada shwarar mu zauna a gida don tsare lafiyar mu. An yi min tarba mai kyau a ofishin DSS. Ba wai don ni ne ba ko ku, sai dai don tsare jihar. Mu kasance lafiya."

An yi kokarin ji ta bakin Ms Ahmad sai dai hakan ya ci tura domin wayar ta a kashe ya ke a lokacin hada wannan rahoton.

Matasa Sun Fita Gari Sunyi Zanga-Zanga Kan Yawaitar Kashe-Kashe a Arewa

Tunda farko, kun ji cewa matasa sun fita titunan wasu garuruwa a arewacin Najeriya suna zanga-zanga kan yawaitar kashe-kashe a yankin, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

'Yan Banga a Kaduna sun fita zanga-zanga kan kama kwamandansu

Duk da cewa a yanzu ana fama da matsalar rashin tsaro a sassan Najeriya da dama, yan ta'adda da yan bindiga sai kara kai hare-hare suke yi duk da kokarin da gwamnati ke yi na kawo karshen su.

An hangi masu zanga-zangar dauke da takardu a jihohin Kano, Bauchi, Zamfara da Sokoto, rahoton Daily Trust.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Online view pixel