Sarkin Musulmi ya koka, yace 'yan ta'adda na kashe jama'ar arewa kowacce rana
- Sarkin musulmi, Muhammadu Sa’ad Abubakar ya koka akan yadda ‘yan bindiga suke halaka jama’a kullum a arewacin Najeriya
- A cewarsa, kisan ya fi tsananta ne a yankin arewa maso yamma duk da dai ba kowanne kisa ne ake bayyanawa ba
- Yayin da sarkin musulmin ya ke jawabi a taron NIREC, ya ce babu ranar da za ta wuce da ba za a halaka dan Adam ba a arewa, wasu ba a samun labari
Sarkin musulmi, Muhammadu Sa’ad Abubakar ya koka akan yadda ‘yan bindiga a kullum suke halaka mutane a arewacin Najeriya musamman a arewa maso yamma duk da dai ba kowanne kisa ake fadi ba.
Wannan ya biyo bayan kiran da Sultan din ya yi wa Kiristoci akan wani razanarwar da wasu da ba a san su ba su ka yi musu, inda suka ce su dakata da zuwa coci a jihar Zamfara ko a halaka su, Tribune Online ta ruwaito.
Yayin jawabi a taron wata ukun karshen shekarar 2021 na kungiyar hadin kan addinai (NIREC) mai taken, ‘Jami’an tsaro da zaman lafiya a Najeriya’ wanda Sultan din ne shugaban NIREC, ya ce babu ranar da za ta wuce ba a halaka mutane ba a arewa.
Ya shaida cewa:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
“Idan muka cigaba da magana akan rashin tsaron da ke arewa, ba za mu bar dakin taron nan ba. Kwanaki kadan da suka gabata mu ka samu rahoto akan matafiyan da aka halaka a cikin mota, duk da dai har yanzu ba a san yawansu ba amma kowacce rai ta na da muhimmanci.
"Babu ranar da za ta wuce ba a halaka mutane ba a arewa musamman a arewa maso yamma, amma ba ma jin labarin kowanne.
“Lokacin da na ga wasikar da ‘yan bindiga su ka yi wa kiristoci barazana a Zamfara, na tambayi amfanin jami’an tsaro a kasar nan. Saboda me zai sa su fito su na yi wa jama’a barazana.
“Ba za mu daina zuwa masallaci ba saboda an yi mana wasikar barazana, ai dole kowa ya mutu, don haka idan kiristoci su ka daina zuwa coci saboda tsoron kada wani da ba su sani ba ya halakasu ai an yi shirme.”
A cewarsa, Najeriya ta na fama da matsalolin rashin tsaro kuma idan shugabanni ba su farka sun gane matsalar da ke gabanmu ba kullum kara tabarbarewa tsaron zai dinga.
Tribune Online ta ruwaito cewa, ya ce kada a ci gaba da yaudarar kai da sunan komai lafiya lau yake. A cewarsa ya dade yana fadin hakan, dole a dage don kawo gyara.
Ya kara da janyo hankalin shugabannin addinai akan sanin abubuwan da za su dinga fada wa mabiyansu don duk abinda suka ce kowa na ganin kamar daga littafi mai tsarki ya zo.
Don haka a daina yaudarar kawuna kuma duk abinda mutum zai fadi ya tabbatar ya na da cikakken ilimi a kansu.
Sultan din ya kara da jan hankali akan tattaunawa don samun maslaha inda ya ce hakan ne kadai mafita.
Ya kara da cewa shugabanni ne matsalar kasar nan, don suna yin abubuwa yadda suka ga dama ba tare da tattaunawa da mabiyansu don jin ta bakinsu ba.
Asali: Legit.ng