Shugaba Buhari ya yi sammako, ya sauka a filin jirgin sama na jihar Legas
- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dira jihar Legas domin bude wasu ayyukan jirage a cikin jihar
- Shugaban ya sauka a filin jirgin Murtala Muhammed ne da sanyin safiyar yau Alhamis 9 ga watan Disamba
- Kafin isar shugaba Buhari Legas, hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar ta bayyana ka'dojin hanya
Legas - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sauka jihar Legas a yau Alhamis, Channels Tv ta ruwaito.
Buhari ya sauka a masaukin shugaban kasa na filin tashi da saukar jiragen sama na Murtala Muhammed da ke Legas da sanyin safiyar yau Alhamis.
Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu da wasu jami’ai ne suka tarbi shugaban a filin jirgin.
A yayin ziyarar, ana sa ran Buhari zai kaddamar da jiragen ruwa da jirage masu saukar ungulu tare da halartar taron kaddamar da littafin tsohon shugaban jam'iyyar APC, Bisi Akande, a cewar Independent.
Kafin ziyarar ta ranar Alhamis, hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Legas (LASTMA) ta ba da shawarar daidaita zirga-zirgar ababen hawa a jihar.
A cikin wata sanarwa da LASTMA ta fitar, ta ce:
"Hanyar Ahmadu Bello, daga Mahadar Adeola Odeku zuwa Adetokunbo Ademola ta Eko Hotels Roundabout za a rufe ta na wani dan lokaci daga zirga-zirgar ababen hawa kuma an karkatar da ababen hawa zuwa Adeola Odeku, Akin Adesola domin hada inda suke son zuwa.
“Akin Adesola mai hade da hanyar Ahmadu Bello da IMB za a rufe ta na wani dan lokaci daga zirga-zirga sannan kuma za a karkatar da ababen hawa zuwa Oyin Jolayemi, Oko Awo da Sanusi Fafunwa domin hada wuraren da suke son zuwa."
Hakazalika, ta kara da cewa, daga Ozumba Mbadiwe (Civic Centre) zuwa Adetokunbo Ademola zuwa Eko Hotels za a karkatar da zirga-zirgar ababen hawa na wani dan lokaci bayan Eko Hotels Roundabout zuwa:
i) Ajose Adeogun,
ii) Sanusi Fafunwa ko kuma koma ta
iii) Civil Center don hada inda suke son zuwa.
Sanarwar ta kara da cewa:
"Dukkan titin da ke kusa da titin Ahmadu Bello daga Mahadar Adeola Odeku, da kuma wadanda ke kan hanyar zuwa Eko Hotels, daga Adetokunbo Ademola Roundabout (Eko Hotels Roundabout), za a rufe su na wani dan lokaci daga zirga-zirga tun da sanyin safiyar ranar Alhamis 9 ga Disamba, 2021."
Shugaba Buhari ya jajantawa iyayen daliban da suka mutu a hatsarin mota a Legas
A baya kunji cewa, shugaba Buhari na Najeriya ya jajantawa iyayen daliban da hatsarin babbar mota ya afkawa a wani yankin jihar Legas.
A jiya ne aka samu afkuwar wani mummunan hatsarin babbar mota, lamarin da yayi sanadiyar mutuwar dalibai biyu da jikkatar wasu 12.
Lamarin ya jawo nuna fushi daga wasu mazauna yankin, inda suka bukaci 'yan sanda su mika musu direban motar.
Asali: Legit.ng