Uwargida ta waskawa miji mari ana tsakiyar shirin ma'aurata a gidan Rediyo, bidiyo

Uwargida ta waskawa miji mari ana tsakiyar shirin ma'aurata a gidan Rediyo, bidiyo

  • Uwargida ta waskawa mijinta mari a gidan rediya a ana tsakiyar shiri
  • Har masu jagorantan shirin sun bude baki don mamaki bisa abinda matar tayi
  • Matar tace tace koda yaushe mijin nata na kokarin bata kunya a bainar jama'a.

Shirin ma'aurata ya sauya zani a kasar Ghana yayinda matar wani mutumi tayi abinda babu wanda yayi tsammani.

An gayyaci wata mata da mijinta shirin sulhu tsakanin ma'aurata a tashar adom1063fm amma matar ta waskawa mijin mari saboda yayi wani magana da bai mata dadi ba ana tsakiyar shirin duniya na kallo.

Mutumin ya tuhumi matarsa da yawan kazanta inda yace tana ajiye fitsari da ba haya cikin daki.

Hakan bai yi mata dadi ba inda ita kuwa ta daukeshi da mari

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: Mutane sun yi gudun mutuwa yayin da wata kotu ta rushe ana tsaka da zaman Shari'a

Tace koda yaushe mijin nata na kokarin bata kunya a bainar jama'a.

Kalli bidiyon:

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel