Ba ni na bada umarnin korar shugabannin Kamfanin wutar lantarki a Abuja ba, Buhari

Ba ni na bada umarnin korar shugabannin Kamfanin wutar lantarki a Abuja ba, Buhari

  • Shugaba Buhari ya musanta rahoton dake cewa ya bada umarnin korar shugabannin kamfanin wutar lantarki a Abuja
  • A wata sanarwa da kakakin shugaban, Malam Garba Shehu, ya fitar, yace kamfanin lantarki ya bar hannun gwamnati tun 2013
  • Yace shugaban ƙasa bai taba nufin yin katsalandan kan harkokin kasuwanci masu zaman kan su ba

Abuja - Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya musanta rahoton cewa ya bada umarnin korar shugabannin kamfanin wutar lantarki a Abuja (AEDC), kamar yadda Tribune ta ruwaito.

A wata sanarwa da kakakin shugaban, Malam Garba Shehu, ya fitar, yace labarin wanda ake jingina shi ga karamin ministan wutan lantarki, cewa shugaba Buhari ya kori da maye gurbin shugabannin ba gaskiya bane.

Shugaba Buhari
Ba ni na bada umarnin korar shugabannin Kamfanin wutar lantarki a Abuja ba, Buhari Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

A sanarwan da Shehu ya fitar, yace:

"Wannan labarin ba zai taba zamowa gaskiya ba, tun da gwamnati ta siyar da kamfanin wutar lantarki ga yan kasuwa a 2013, shugabannin sun koma hannun sabbin masu iko da kamfanin."

Kara karanta wannan

Ana yi wa Shugaban kasa martani a kan zuwa Legas, ana makokin mutum 80 a Sokoto

"Dan haka ba hurumin gwamnati bane kuma ba dai-dai bane a jingina wa shugaban kasa kamfanin kuma har ace ya sallami shugabanni."
"Mun yi farin ciki domin shi kanshi ministan da aka jingina wa rahoton ya nesanta kansa da lamarin."

Ba hannun shugaba Buhari

Sanarwan ta cigaba da cewa fadar shugaban ƙasa na tabbatarwa masu hannun jari a kamfanin cewa shugaba Buhari bai bada umarnin sallaman shugabannin ba, Premium times ta ruwaito.

"Shugaba Buhari ba shi da hannu kuma bai taba nufin yin katsalandan game da harkokin kasuwanci masu zaman kan su ba."
"Fadar shugaban kasa na maraba da tattaunawar da ake yi da masu ruwa da tsaki domin shawo kan matsalolin da suka taso kan wannan lamarin."

A wani labarin na daban kuma Shugaba Buhari ya yi Allah wadai da kisan ɗalibin makarantar Dowen, Sylvester Oromoni, dake jihar Legas

Kara karanta wannan

Uwargida ta waskawa miji mari ana tsakiyar shirin ma'aurata a gidan Rediyo, bidiyo

Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari , ya tabbatar da cewa doka zatai aiki a kan duk wani mai hannu a kisan ɗalibin kwalejin Dowen, Sylvester Oromoni.

Ya bayyana cewa a yan kwanakin nan , ƙasar nan ta girgiza da mummunan lamarin da ya faru a kwalejin Dowen dake jihar Legas.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262