Kudin Makamai: EFCC ta gurfanar da Tsohon Shugaban Sojoji kan almundahanan kimanin N14bn

Kudin Makamai: EFCC ta gurfanar da Tsohon Shugaban Sojoji kan almundahanan kimanin N14bn

  • An bankado yadda manyan hafsosin Soji suka wawure kudin makaman da gwamnatin tarayya ta basu
  • Hafsoshin Sojin mutum uku kadai sukayi babakere da kudi kimanin bilyan goma sha hudu
  • An bukaci hukumar Soji ta mika mata wadannan Sojoji uku don a gurfanar da su gaban kuliya

Hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa watau EFCC ta shigar da tsohon babban hafsan Sojin Najeriya, Kenneth Minimah, kan laifin babakeren N13bn na makamai.

An shigar da Minimah ne tare da shugaban kasafin kudin hukumar Soji, Manjo Janar A. O Adetayo da tsohon diraktan kudi na hukumar, Birgediya Janar R. I Odi.

An kai kararsu ne babban kotun tarayya dake birnin tarayya Abuja, rahoton Premium Times.

Kudin Makamai: Minimah
Kudin Makamai: EFCC ta gurfanar da Tsohn Shugaban Sojoji kan almundahanan N13bn
Asali: UGC

Kara karanta wannan

Zamfara: Kasurgumin ɗan bindiga, Turji, ya kai mummunan hari hanyar Kauran Namoda-Shinkafi

Rahoton binciken da akayi kansu

Hukumar EFCC ta bayyana cewa ta samu rahoto daga kwamitin binciken kudin makamai daga 2007 zuwa 2015, karkashin jagorancin tsohon Soja, Jon Ode.

Rahoton yace tsakanin 2010 da 2015 hukumar ta karbi makudan kudade amma wasu suka zuba kudaden aljihunsu.

Rahoton yace:

"Biliyoyin Naira da hukumar Soji ta samu daga wajen Gwamnatin tarayya don sayen makami amma an gano wasu manyan Soji suka wawure kudin."
"Mutanen da suka wawure Bilyan goma sha uku (N13,798,619,309) sune tsohon shugaban hafsan Soji, Laftanal Janar Kenneth Miniman; shugaban kasafin kudin hukumar Soji, Manjo Janar A. O Adetayo da tsohon diraktan kudi na hukumar, Birgediya Janar R. I Odi."

Ya akayi da kudaden

Rahoton ya cigaba da cewa:

"An tura wadannan kudaden daga baitul malin Soji zuwa asusun bankunan kamfanonin wadannan mutane da basu da wata alaka ta kasuwanci da hukumar Soji."
"Hukumar Soji da Gwamnatin tarayya sun yi asara matuka sakamakon riban da wadannan hafsoshin sukayi da kudaden nan don amfanin kansu."

Kara karanta wannan

2023: Ta kacame tsakanin gwamnonin APC kan batun fitowa takarar Tinubu

EFCC tace sakamakon wannan bincike, ta rubuta wasika ga hukumar Soji ta mika mata wadannan Sojoji uku don a gurfanar da su, kuma ya kamata ace an yi tun Satumban 2020.

Shugaban ICPC ya tono kwangilolin da aka ba Sanatan APC, ya kai wa Buhari hujjoji

Hukumar ICPC mai yaki da marasa gaskiya a Najeriya, ta gano yadda wasu ‘yan majalisa suka hada-kai da hukumomin gwamnati, suka karbi kwangiloli.

Jaridar Daily Nigerian tace binciken na ICPC ya fallasa yadda musamman Sanatan Kano ta Arewa, Barau Jibrin ya tashi da wasu kwangiloli na biliyoyin kudi.

Cikin kwangilolin da aka gano an ba Sanata Barau Jibrin akwai wani aiki da kamfanin Sinti Nig. Ltd ya samu, wanda ‘dan majalisar ne shugaban wannan kamfani.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng