Buhari ya sha alawashin ladabtar da masu daukar aikin gwamnati ba bisa ka'ida ba

Buhari ya sha alawashin ladabtar da masu daukar aikin gwamnati ba bisa ka'ida ba

  • Shugaba Buhari ya dauka alkawarin daukar matakin ladabtarwa kan masu daukar aikin gwamnati ba bisa ka'ida ba
  • Buhari ya koka da yadda wasu ma'aikatu ke bayyana tsoffin ayyuka a matsayin sabbi a kasafin kudinsu, kuma ya ce tabbas za a yi maganinsu
  • Kamar yadda Buhari ya bayyana, ya ce gwamnatinsa ta dauka matakin dakile waddaka da kudi ta hanyar karasa ayyukan da gwamnatocin baya suka yi watsi da su

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sha alwashin daukan mataki tsatsaura kan duk wasu ma'aikatan gwamnati da ke da hannu wurin take dokokin gwamnatin tarayya ta hanyar daukar aiki ba bisa ka'ida ba tare da rufe ma'aikatan bogi.

Shugaban kasa Buhari wanda ya yi jawabin ne a taron bajekoli karo na uku na yaki da rashawa a fannin ayyukan gwamnati, wanda hukumar yaki da rashawa mai zaman kanta ta (ICPC) tare da hadin guiwar ofishin sakataren gwamnatin tarayya suka shirya.

Kara karanta wannan

Buhari ya kai wasika majalisa, ya nemi a amince da kudirin kudin 2021 kafin 2022

Buhari ya koka kan yadda ake daukar aikin gwamnati ba bisa ka'ida ba tare da rufe asirin ma'aikatan bogi wanda ya janyo hauhuwar kudin da gwamnati ke kashewa wanda ke illa ga tattalin arzikin kasar nan.

Hotuna cikin labari: Buhari ya halarci taron yaki da rashawa a ma'aikatun gwamnati
Hotuna cikin labari: Buhari ya halarci taron yaki da rashawa a ma'aikatun gwamnati. Hoto daga ICPC Nigeria
Asali: Facebook

Shugaban kasan ya kara da koka wa kan yadda ma'aikatu, sassa da cibiyoyin gwamnati ke kwafar ayyuka wanda hakan ke kara nauyi kan kudin shigar gwamnatin tarayya. Ya sha alwashin cewa shugabannin ma'aikatun za su fuskanci hukunci.

Buhari ya nuna jin dadinsa kan yadda mahukunta da fannin shari'a suke kokarin zabtare yawan kudaden da ake kashewa, daidaita kudaden da gwamnati ke kashewa alhakin kowa ne ba wai wadanda aka zaba kadai ba.

Ya kara da yin bayanin yadda gwamnatinsa ta zabtare yawan kudin da ake kashewa inda ta mayar da hankali kan ayyukan da gwamnatin baya ta yi watsi da su tare da wadanda ake yi a halin yanzu.

Kara karanta wannan

Ku kara kaimi wajen fatattakar yan ta'adda a Najeriya, Shugaba Buhari ga Sojoji

Ya jaddada cewa, daga binciken ICPC, an gano cewa wasu ma'aikatun sun dauka hanyar amfani da hanyoyin gabatar da ayyukan da ake yi a matsayin sabbin ayyuka, daukar aiki ba bisa ka'ida ba tare da rufawa ma'aikatan bogi asiri.

Ya ce:

"Wadanda ke daukar ma'aikata ba bisa ka'ida ba kuma suke boye ma'aikatan bogi, dole ne a zakulo su tare da ladabtar da su.
"Mun tabbatar da cewa ma'aikatu basu kawo sabbin ayyuka ba a madadin wadanda ake aiwatarwa. Gwamnati ta gano ta hanyar ICPC cewa wasu ma'aikatu sun dauka hanyar damfara ta yadda suke gabatar da tsoffin ayyuka a matsayin wadanda za su yi.
"Shugabannin wadannan ma'aikatun da aka kama da laifukan za su fuskanci hukunci. Ina da tabbacin cewa ICPC za ta cigaba da sa idon da ya dace."

Ayyuka 257 aka kwafo daga kasafin kudin 2021 masu darajar N20bn, ICPC

A wani labari na daban, Bolaji Owasanoye, shugaban hukumar yaki da rashawa mai zaman kanta, ICPC, ta ce ayyuka 257 da za su kai darajar N20.138 biliyan aka kwafa daga kasafin kudin shekarar 2021.

Kara karanta wannan

Hankula sun tashi yayin da buhun siminti ya kai N4,600 a Najeriya

Shugaban hukumar ICPCn yayin jawabi a taro karo na uku kan disashe rashawa a aikin gwamnati a kasar nan mai taken “Corruption and the Cost of Governance: New Imperatives for Fiscal Transparency”, ya ce hukumar ta bibiyi ayyuka 1083 a fadin kasar nan ban da Borno da Zamfara saboda matsalar tsaro, TheCable ta ruwaito.

TheCable ta ruwaito cewa, ya sanar da cewa yayin binciken, ICPC ta tirsasa 'yan kwangila 67 sun koma aikin kuma sun tabbatar da kammaluwar ayyuka 966 masu darajar N310 biliyan wadanda aka watsar a baya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng