Buhari ya kai wasika majalisa, ya nemi a amince da kudirin kudin 2021 kafin 2022
- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika wata wasika gaban majalisar dattawa domin neman a amince da bukatarsa
- Shugaban ya bayyana bukatar majalisa ta amince da kudurin kasafin kudi na 2021 wanda zai tallafi kasafin kudin 2022
- Shugaban ya mika wasikar ne, wacce shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan ya karanta a zauren majalisar dattawa
Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rubutawa majalisar dattawa wasika, inda ya nemi a duba tare da amincewa da kudirin kasafin kudin shekarar 2021 wanda zai jagoranci aiwatar da kasafin 2022.
A wasikar dai shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan ya karanta yayin zaman majalisar a ranar Talata 7 ga watan Disamba, Vanguard ta ruwaito.
Shugaba Buhari ya ce kudirin idan aka amince da shi zai taimaka wajen tallafawa kasafin 2022 na bunkasar tattalin arziki da dorewarta da ke gaban majalisar dokokin kasar, inda ake jiran amincewa da shi.
A cewar shugaban, kudirin dokar zai kuma taimaka wajen aiwatar da wasu sauye-sauye a harkokin kudi na gwamnati.
Kudirin ya ba da shawarar yin gyare-gyare daban-daban ga dokokin haraji da ake da su da kuma ka'idojin kudi don daukar mataki a tasirin cutar ta Korona kan tattalin arziki da koma bayan tattalin arziki na yanzu.
Wasikar shugaban ta ce:
"A bisa sashe na 58 da 59 na kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya na shekarar 1999 (wanda aka yi wa kwaskwarima), na bukaci majalisar dattijai ta duba kudirin kasafin kudin shekarar 2021 domin amincewa dashi.
"Kudirin Kudi na 2021 zai tallafawa aiwatar da kasafin 2022 na Tarayya don Ci gaban Tattalin Arziki da Dorewarsa ta hanyar ba da shawarar yin gyare-gyare ga fannin haraji, hukumar kwastam, kasafin kudi da sauran dokoki da suka dace.
“Musamman, wannan Kudirin ya tanadi inganta yunkurin tattara kudaden shiga na cikin gida don kara yawan tara haraji da kudaden shiga ba tare da haraji ba, Tafiyar da Haraji da Gyaran Majalisun Dokoki, musamman don tallafawa sauye-sauyen da ake samu ta kai tsaye na Hukumar Kula da Harajin Cikin Gida ta Tarayya (FIRS).”
An nada shugaba Buhari shugabancin wata babbar kungiya a Afrika ta PAGGW
A wani labarin, shugaba Muhammadu Buhari ya karbi ragamar shugabancin kungiyar Pan African Great Green Wall (PAGGW), a Afirka, kamar yadda karamar minista a ma'aikatar muhalli, Mrs Sharon Ikeazor, ta sanar a ranar Lahadi a Abuja.
Sanarwar da Daraktan Yada Labarai na Ma’aikatar Sagir el Mohammed ya fitar ta ce Najeriya ta karbi ragamar mulkin ne a karshen taron shugabannin kasashe da gwamnatocin PAGGW karo na 4 da aka gudanar a ranar 2 ga watan Disamba a Abuja.
A cewar ministar:
“A karshen taro na 4 na CHSG, Najeriya ta karbi shugabancin kungiyar PAGGW."
Asali: Legit.ng