Dangote ya fi kasashe 30 na Afrika arziki bayan tashin farashin simintin kamfaninsa

Dangote ya fi kasashe 30 na Afrika arziki bayan tashin farashin simintin kamfaninsa

  • Har yanzu Aliko Dangote na cigaba da hawa matattakalar attajiran duniya inda ya tara dukiyar da ta fi ta kasashen Afirka da dama
  • Dukiyarsa ta karu bayan kamfanoninsa na siminti da taki sun samu karbuwa kwarai, hakan ya sa arzikinsa jimilla ya dagu yayi sama
  • Yadda dan kasuwar ya fara kasuwancinsa ta hanyar ba wa matasa kwarin guiwa ce amma dai mutane da dama sun ce gwamnatin kasar nan ta dafa masa

Dukiyar mai kudin Afirka, Aliko Dangote, ta karu da naira tiriliyan 8.4 sakamakon yadda ake tururuwar siyan siminti da takinsa.

Bisa rahoton Bloomberg, dukiyarsa ta karu da dala biliyan 20.1 wanda ya yi daidai da naira tiriliyan 8.4 a ranar Juma’ar da ta gabata.

Kara karanta wannan

Hankula sun tashi yayin da buhun siminti ya kai N4,600 a Najeriya

Dangote ya fi kasashe 30 na Afrika arziki bayan tashin farashin simintin kamfaninsa
Dangote ya fi kasashe 30 na Afrika arziki bayan tashin farashin simintin kamfaninsa. Hoto daga bloomberg.com
Asali: UGC

Yanzu haka dukiyar Dangote gaba daya ta kai dala biliyan 26.27 daidai da naira tiriliyan 11 wanda ya kai a 2014.

Dangote ya kai matakin arzikin da zai taba iya samu cikin shekaru 7 a 2021, kuma hakan ya biyo bayan kamfaninsa na siminti da tsadar siminti ta karu.

Har ila yau, kudin mai sun taimaka wa dukiyarsa har suka kara daga naira tiriliyan 8.2 a shekarar nan zuwa naira tiriliyan 8.4 ($21.2 biliyan).

Wannan ita ce makurar dukiyar da ya taba kai wa tun daga shekarar 2014, Bloomberg ta ruwaito.

Yawan bukatar siminti da kuma karin tsadar kayan gini a Najeriya sun kara wa kamfanin simintin Dangote yawan kudin shiga, kuma kamfanin na cikin manyan kadarorinsa.

Kara karanta wannan

Abokan aiki na dariya suka rika min: Matar da ta ajiye aikin ɗan sanda ta rungumi noma

Aliko, mai shekaru 64 ya kusa cikasa dala biliyan 19 (N17.8 tiriliyan) na matatarsa wacce za ta iya samar wa da Najeriya duk wasu kayan man fetur da za a bukata.

Yanzu haka ya fara tura taki zuwa Amurka da Brazil tun bayan kammala kamfaninsa na taki mai iya samar da ton miliyan 3 na Urea da Ammonia duk shekara.

Da dama cikin kasashe 54 da ke nahiyar Afirka ba su kai arzikin Dangote ba, inda kasashen 20 kadai ne su ka fi shi arziki.

Yanzu haka zai zama mutum na 21 a jerin kasashe masu arziki da ace Dangote kasa ne shi kanshi, kamar yadda VON suka kiyasta.

Ya fi kasashe irinsu Burundi, Somalia, Burkina Faso, Central African Republic, Mozambique da sauransu tarin arziki.

Dama an haifi Dangote ne a cikin dangin ‘yan kasuwa kuma musulmai na arewa.

Ya fara sana’ar siyar da siminti tun ya na da shekaru 21. Ya koma siyar da kayan gine-gine a shekarar 1990 da doriya.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Al'amarin ya isa haka, Matasan arewa sun fara yi wa Buhari bore

Gwamnati ta tallafa masa kwarai yayin da ta dakatar da shigo da wasu kaya da dama kasar nan. An zarge shi da amfani da damar da ya samu daga gwamnatin wurin azurta kansa, zargin da ya dade yana musawa.

Hankula sun tashi yayin da buhun siminti ya kai N4,600 a Najeriya

A wani labari na daban, jaridar The Guardian ta bayyana yadda farashin kaya suka ninku ciki har da siminti da kayan gine-gine a kasuwannin kasar.

Kamar yadda rahoton ya nuna, karin tsadar kayan gine-gine yana janyo tsadar gidaje sakamakon kudaden da ake narkawa wurin ginasu.

An shawarci gwamnatin Buhari ta yi wani abu wurin dakatar da hauhawar farashin kaya a cikin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng