WHO: Kimanin kashi 1 bisa 3 na wadanda Maleriya ta kashe a 2020 a duniya yan Najeriya ne

WHO: Kimanin kashi 1 bisa 3 na wadanda Maleriya ta kashe a 2020 a duniya yan Najeriya ne

  • Hukumar Lafiya ta Duniya ta sanar da cewa, kashi daya bisa ukun mace-macen da aka samu sakamakon cutar maleriya a duniya duk a Najeriya ta faru
  • Kamar yadda rahoton WHO ya bayyana, annobar cutar korona ta taka rawar gani wurin dakile magance cutar zazzabin cizon sauro a duniya
  • WHO ta sanar da cewa, kashi 50 na mace-mace da masu cutar zazzabin cizon sauro na shekarar 2020 suka yi an same su ne a nahiyar Afrika

Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, ta ce kasashe shida ne da suka hada da Najeriya suke da kashi hamsin na dukkan mace-macen da aka yi a duniya sakamakon zazzabin cizon sauro a 2020.

Hukumar ta bayyana hakan ne a rahoton zazzabin cizon sauro da ta saki a ranar Litinin kamar yadda TheCable ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Annobar da ta fi Koronar farko na tunkaro duniya, kowa ya shirya inji masana

Kamar yadda rahoton WHO ya bayyana, kiyasi ya nuna an samu masu cutar har 241 miliyan kuma an samu mace-mace 627,000 na masu cutar wadanda da yawa daga cikinsu yara ne kanana masu shekaru kasa da biyar a duniya a shekarar 2020.

WHO: Kimanin kashi 1 bisa 3 wadanda Malariya ta kashe a 2020 a duniya yan Najeriya ne
WHO: Kimanin kashi 1 bisa 3 wadanda Malariya ta kashe a 2020 a duniya yan Najeriya ne. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Kiyasin shekarar 2020 ya bayyana kusan karin miliyan 14 idan aka danganta da na shekarar 2019 inda aka samu mace-macen rayuka 69,000.

A rahoton, Najeriya tana daga cikin kasashe shida da jimillar wadanda suka yi fama da cutar zazzabin cizon saura a duniya ya kai kashi 55 na duniya.

"Kusan 96% na mace-macen maleriya a duniya sun faru ne a kasashe 29. Kasashe shida - Najeriya tana da 27% Jamhuriyar Kongo ta na da 12%, Uganda tana da 5%, Mozambique tana da 4%, Angola tana da 3% da Burkina Faso mai 3%. Jimillar hakan ne ya kai rabin dukkan masu cutar da aka samu a fadin duniya a 2020," rahoton yace.

Kara karanta wannan

An tura dakarun Sojoji Najeriya kasar Mali don tabbatar da zaman lafiya

"Kasashe 29 na duniya ne aka samu 96% na masu cutar zazzabin cizon sauro a duniya kuma kasahe shida na sama su ne, Najeriya ta na da 27%, jamhuriyar Kongo tana da 12%, Uganda ta na da 5%, Mozambique tana da 4%, Angola tana da 3.4% da Burkina Faso mai 3.4%," ya kara da cewa

Kamar yadda rahoton ya nuna, annobar korona ta dakile magance cutar zazzabin cizon sauro, lamarin da ya kawo yawan mace-mace da kuma masu kamuwa da cutar, TheCable ta ruwaito.

Kamar yadda takardar da WHO ta fitar, lamarin na iya kazanta domin a kasashen Afrika, an daina samun dakile sauran cutuka sakamakon hankali da ya koma kan annobar korona.

Darakta janar na WHO, Tedros Ghebreyesus ya ce rahoton maleriya na wannan shekarar ya duba barnar da cutar korona ta yi a duniya wurin hana duban hatsarin cutar maleriya.

Jerin Kasashen da Suka Mance da Labarin Maleriya Tsawon Shekaru 20

Kara karanta wannan

Jerin kasashe 14 da gwamnatin Saudiyya ta haramtawa shiga kasarta saboda Korona

A wani labari na daban, an yi bikin yaki da cutar zazzabin cizon sauro da aka fi sani da Maleriya, cutar da ke da alhakin hallaka dubban mutane musamman kananan yara a duniya.

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta bayyana cewa, a duk minti daya zazzabin cizon sauro na kashe yaro daya a duniya.

WHO ta bayyana haka ne a yayin da ake bikin ranar yaki da cutar zazzabin ciwon sauro ta duniya. Hukumar ta ce a shekarar 2019 cutar zazzabin cizon sauro da aka fi sani da maleriya ta kashe kusan mutum 400,000 a kasashe 87, kuma ta fi kashe yara 'yan kasa da shekara biyar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng