Da dumi-dumi: 'Yan bindiga sun bindige wani malamin kwaleji a jihar Benue
- Wasu 'yan bindiga sun bindige wani malamin kwaleji a jihar Benue a kan hanyarsa ta komawa inda yake aiki
- Matasa a yankin sun fito sun zanga-zanga don nuna damuwarsu da yawaitar hare-hare a yankin a jihar Benue
- Hukumar 'yan sanda ta ce bata samu kabari ba, amma tana ci gaba da gudanar da bincike kan faruwar lamarin
Benue - Wasu 'yan bindiga sun bindige wani babban malami a kwalejin kimiyya da fasaha ta jihar Benue da ke Ugbokolo a yammacin jiya Lahadi a sashin Eke na hanyar Otukpo zuwa Enugu a karamar hukumar Okkwu na jihar Benue.
Marigayin malamin, mai suna Adah Echobu Chris, wanda aka fi sani da, “The Bull”, an yi zargin wasu ‘yan bindiga ne suka kai masa hari a lokacin da yake komawa mazauninsa da ke Ugbokolo daga garin Eke, da ke yankin karkara.
Shaidu sun ce malamin yana tuka motarsa ne a lokacin da ‘yan bindigar suka kama shi suka harbe shi har lahira.
Lamarin dai ya janyo zanga-zanga a ranar Litinin inda matasan yankin suka tare hanya na tsawon sa’o’i da dama tare da neman a tsaurara matakan tsaro a yankin.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Wani mazaunin yankin, ya shaida wa Daily Trust ta wayar tarho cewa, bangaren hanyar (Eke – Ugbokolo) ya yi kaurin suna wajen fashi da makami, inda ya jaddada cewa an sha samun aukuwar kisa a yankin.
Mazaunin, wanda ya nuna damuwarsa kan munanan abubuwan da suka faru a yankin duk da kusancinsa da ofishin ‘yan sanda, ya kuma yi zargin cewa ‘yan sanda ba su taba daukar bayanan da ke cewa ‘miyagu’ suna addabar yankin da gaske ba.
Ya ce a bisa haka ne jama’a suka tare hanya domin neman a gaggauta sauya ko kuma a tura sabbin ‘yan sanda zuwa Okpokwu, ya kara da cewa a sauya kwamandan yankin da wani jami’in da ya dace.
Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Catherine Anene, ta tabbatar da faruwar lamarin inda ta ce wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne suka harbe marigayin, ini rahoton Punch.
Hukumar jami'a ta kori lakcarorinta 4 bisa karbar kudi ta bayan fage da rashin da'a
A wani labarin, hukumar gudanarwar jami’a mallakin jihar Edo ta Ambrose Alli (AAU) da ke Ekpoma, ta amince da korar wasu lakcarorin jami’ar guda hudu bisa zarginsu da rashin da’a.
An amince da korar tasu ne a taron gaggawa na kungiyar shiga tsakani na musamman (SIT), wanda aka gudanar a ranar Laraba 1 ga Disamba, 2021.
A taron na gaggawa, an yi la’akari da rahoton kwamitin ladabtarwa na manyan ma’aikata (SSDC) kan zargin da ake yi wa lakcarori hudu da aka kora.
Asali: Legit.ng