Innalillahi: Garin rage mata hanya, an sace yarinya mai shekaru 5 a jihar Kano
- Wasu masu garkuwa da mutane sun sace wata yarinya mai shekaru 5 a jihar Kano a hanyarta ta dawowa daga Islamiyya
- Rahoto ya bayyana cewa, wasu mutane ne a cikin babur din a dai-daita sahu suka sace yarinyar da sunan rage mata hanya
- Wani danginta ya bayyana yadda yara a unguwar ke zuwa makaranta, inda ya bayyana bukatarsu ga al'umma baki daya
Jihar Kano - An sace wata yarinya ‘yar shekara biyar mai suna Hanifa Abubakar a unguwar Kawaji da ke Kano a ranar Asabar.
Masu garkuwa da mutane ne suka yi awon gaba da ita a cikin babur din dai-daita sahu yayin da suka yaudare ta da sunan rage hanya
Daily Nigerian ta tattaro cewa lamarin ya faru ne da karfe 5 na yamma lokacin da yarinyar da sauran yaran unguwar suke dawowa daga makarantar islamiyya.
Kawunta, Suraj Zubair ya ce:
Kawunta, Suraj Zubai ya ce:Kawunta, Suraj Zubai ya ce:
“Nisan dake tsakanin gidansu zuwa makarantar Islamiyya bai da yawa. Don haka yara sukan yi tattaki zuwa makaranta da kansu.
“A cewar wasu yaran da lamarin ya faru a gaban idanunsu, masu garkuwa da mutanen sun zo ne a cikin a dai-daita sahu suka ce za su kai su gidansu. Bayan saukarsu ne suka ce Hanifa ta sake shiga domin sake dana ta, daga nan suka tsere da ita.
“Ina so in yi amfani da wannan kafar domin yin kira ga wadanda suke da wani bayani game da inda Hanifa take da su tuntubi ofishin ‘yan sanda mafi kusa ko su kira wannan lambar: 08032668195.”
Unguwar Kawaji a karamar hukumar Nassarawa na daya daga cikin unguwannin da ake fama da matsalar satar yara a Kano.
A cikin unguwar a baya, an yi garkuwa da Yusuf Nasiru dan shekara 9 a ranar 28 ga watan Disamba, 2020 bayan ya dawo daga makarantar Islamiyya da rana.
Idan za a iya tunawa, a watan Oktoban 2019, rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta kama wasu gungun masu garkuwa da mutane shida bisa zarginsu da yin garkuwa da yara, da sayar da su da kuma tursasa musu karbar addinin kirista a garin Onitsha na jihar Anambra.
Biyo bayan yawaitar sace yaran Kano da aka yi a shekarun baya tare da kubutar da wasu daga cikinsu a Kudancin kasar nan, Gwamna Abdullahi Ganduje ya kafa wani kwamitin bincike.
Manufar kwamitin shi ne ya binciki yadda ake tauye hakkin yaran da aka ceto tare da bankado duk irin wadannan lamura daga shekarar 2010 zuwa yau a jihar.
Kasurgumin mai garkuwa da mutane ya mutu a gidan yari yayin jiran hukunci
A wani labarin, Chiemeka Arinze, wanda ake tuhuma da laifin sace mutane tare da hamshakin attajirin nan mai garkuwa da mutane, Chukwudumeme Onwuamadike, wanda aka fi sani da Evans, ya mutu a gidan yari, Vanguard ta ruwaito.
Evans yana fuskantar shari’a tare da Joseph Emeka, Chiemeka Arinze da Udeme Upong, kan yunkurin yin garkuwa da Cif Vincent Obianodo, shugaban kamfanin Young Shall Grow Motors, a gaban mai shari’a Oluwatoyin Taiwo na wata kotun manyan laifuka ta Ikeja.
Suna fuskantar tuhume-tuhume bakwai da suka hada da kisan kai, yunkurin kisa, hada baki don yin garkuwa da mutane, yunkurin garkuwa da mutane da kuma harkallar da makamai.
Asali: Legit.ng