Matafiya da dama sun makale a yayin da ‘yan bindiga suka tare hanya a Neja

Matafiya da dama sun makale a yayin da ‘yan bindiga suka tare hanya a Neja

  • Wasu hotuna da Channels ta yada sun nuna lokacin da wasu matafiya suka makale yayin da 'yan bindiga suka tare hanya
  • An ruwaito cewa, matafiya da dama sun tsere zuwa wasu kauyuka mafi kusa domin tsoron kada a sace su
  • Daga baya, an ce jami'an tsaro sun zo wurin domin share hanyar da kuma tabbatar tsaron matafiya da masu ababen hawa

Neja - Wasu ‘yan bindiga da ba a tantance adadinsu ba a ranar Asabar sun tare hanyar Kontagora zuwa Minna a jihar Neja, lamarin da ya haifar da cikas a yankin.

Hakan ya sa motoci da matafiya da dama suka makale a kewayen Yakila da Garun Gabas kusa da Kundu a karamar hukumar Rafi.

Yayin da 'yan bindiga suka tare hanya a Neja
Hotunan matafiya da dama da suka makale a yayin da ‘yan bindiga suka tare hanya a Neja | channelstv.com
Asali: UGC

Majiyoyi sun shaidawa gidan Talabijin na Channels cewa rufe hanyar ya dauki kusan awa daya, kuma babu jami’an tsaro da suka zo don share hanyar a yankin a lokacin.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Garin rage mata hanya, an sace yarinya mai shekaru 5 a jihar Kano

An ce matafiya sun tsere zuwa kauyukan da ke kusa da saboda ba za su iya ci gaba da tafiya ba saboda fargabar yin garkuwa dasu daga 'yan bindigan.

Duk da haka, rahotanni sun ce 'yan bindigan sun yi awon gaba da wasu mutane da ba a bayyana adadinsu ba tare da kai su inda ba a sani ba har yanzu.

Sai dai shaidun gani da ido sun ce daga baya tawagar jami’an tsaro ta isa wurin domin share hanyar a wani yunkuri na tabbatar da tsaro ga matafiya da masu ababen hawa.

Wani shaidan gani da ido ya shaidawa majiya cewa:

“Mun kasance a makale na wasu sa’o’i yayin da ‘yan bindiga suka dauki lokacinsu don yin barna. A karshe, an yi garkuwa da wasu adadin mutane. Lamarin ya kasance abin tausayi, yayin da dukanmu muke kallo ba tare da iya taimakawaba."

Kara karanta wannan

Wadanda suka tsere daga gidan yarin Kogi ne ke da alhakin kai hari Masallacin Neja, 'Yan sanda

“Dukkanmu mun ji tsoro domin, babu abin da za mu iya yi. Babu wani jami'in tsaro da ya taimaka mana. Hatta ’yan garin duk sun buya. Muna addu’ar Allah ya taimaki Neja da Najeriya domin kawo karshen wannan lamari.”

'Yan bindiga sun kai wa 'yan sanda wasikar sanarwar kai hari a Zamfara

A wani labarin, rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta tabbatar da cewa ta samu wasikar barazanar kai hari a wani coci-coci a Gusau, babban birnin jihar.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Ayuba Elkanah, ya ce wasu da ba a san ko su wanene ba ne suka jefar da wasikar a hedikwatar ‘yan sandan jihar.

Ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da manema labarai a Gusau ranar Talata, SaharaReporters ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.