Tsagin adawa da Tinubu a Legas sun bar APC, Saraki ya karbe su zuwa PDP

Tsagin adawa da Tinubu a Legas sun bar APC, Saraki ya karbe su zuwa PDP

  • Wani tsagin jam'iyyar APC a jihar Legas ya sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP saboda sabani da Asiwaju Bola Tinubu
  • A ranar Asabar ne Bukola Saraki ya jagoranci 'yan kungiyar Lagos4Lagos zuwa PDP makwanni bayan taron gangaminn jihohi na APC
  • A Legas an gudanar da taron gangamin jihohi, inda aka samu rabuwar kai tsakanin tsagin Tinubu da tsagin LagosLagos

Legas - Wani bangare na jam’iyyar APC a Legas a karkashin inuwar Lagas4Lagos a ranar Asabar din da ta gabata ya sauya sheka zuwa jam’iyyar PDP, Daily Trust ta ruwaito.

Tsohon shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki ya jagoranci kungiyar zuwa jam’iyyar PDP a wani biki da aka gudanar a Legas.

Kungiyar Legas4Lagos a karkashin jagorancin Olajide Adediran, wanda aka fi sani da Jandor, ta sha fafatawa da shugabannin APC a jihar.

Kara karanta wannan

Shugaban APC a Kano Danzago: Gwamna Badaru da Gwamnan Ekiti sun shaida

Jam'iyyar APC
Tsagin adawa da Tinubu a Legas sun bar APC, Saraki ya karbe su zuwa PDP | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Kungiyar ta gudanar da tarukan gangaminta daban a matakan gundumomi, unguwanni da kananan hukumomi da na jahohi na jam’iyyar APC a kwanakin baya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sai dai ba a amince da taron da kungiyar Jandor ta gudanar ba yayin da sakatariyar jam’iyyar ta kasa ta amince da taron da bangaren APC a tsagin Asiwaju Bola Tinubu suka gudanar.

Jandor, wanda ya nuna sha'awar tsayawa takarar gwamna a jihar a zaben 2023, ya jagoranci mambobinsa daga kananan hukumomi 20 na jihar zuwa jam'iyyar PDP a ranar Asabar.

Yayin da yake karbar sabbin 'yan PDP a Legas, Saraki ya tabbatar musu da cewa “sun koma jam’iyyar da za ta ceto Najeriya, zuwa jam’iyyar da za ta ceto jihar Legas, zuwa jam’iyyar da za ta sauya arzikin kasar nan.”'

A bangaren APC har ila yau, daya tsagin kwamitin tsare-tsare na taron gangami na musamman (CEPC) a jam’iyyar APC mai mulki a ranar Litinin da ta gabata, ya yi zargin cewa wasu jiga-jigan jam’iyyar ‘yan jam’iyyar adawa ta PDP ne.

Kara karanta wannan

Lokacin mu ne: ‘Dalibin Jami'a mai shekara 28 zai yi takarar Shugaban matasa a Jam’iyyar APC

Kwamitin ya kuma ce suna sanya rigar jam’iyyar APC mai mulki ne kawai don su lalata kudurin jam'iyyar.

Daily Trust ta ruwaito cewa kungiyar Progressive Youth Movement (PYM) ta kaddamar da sabon kwamitin CEPC a Abuja, a ranar Litinin.

Sai dai kwamitin Buni ya mayar da martani nan take, yana mai cewa matasan ma jam’iyyar bata san su ba, don haka tsageru ne kawai.

Da yake mayar da martani, Shugaban sabon kwamitin na CECPC, Prince Mustapha Audu, ya ce matasan ‘ya'ya ne ga jam’iyyar kuma masu dauke da katin rajista kuma sun hidimta mata.

Zan koya wa sauran jam'iyyun siyasa mummunan darasi a 2023, gwamnan Adamawa

A wani labarin, Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri na jihar Adamawa ya ce zai koyar da sauran jam’iyyun siyasa a jihar munanan darrusa a zaben 2023 mai zuwa.

Daily Trust ta ruwaito cewa, Fintiri ya bayyana haka ne a lokacin amincewarsa da kungiyar kansilolin jihar Adamawa a dakin liyafa na gidan gwamnati da ke Yola a ranar Laraba 1 ga watan Disamba.

Kara karanta wannan

Rikicin Goje da Inuwa: Kotu ta tasa keyar hadimin Goje zuwa kotu saboda yin rubutu a Facebook

An jiyo gwamnan jihar Adamawa yana cewa: "Sun gaza a cikin shekaru hudu da suka samu damar gudanar da mulkin jihar, kuma ba za mu bar su su yaudari jama'armu ba, za mu ci gaba da yin aiki tukuru, mu samar da romon dimokuradiyya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.