Jerin kasashe 14 da gwamnatin Saudiyya ta haramtawa shiga kasarta saboda Korona
A makon nan ne aka samu bullar sabon nau'in Korona na Omicron, wanda hukumar lafiya ta duniya (WHO) tace nau'i ne mai tsananin hadarin gaske.
Kasashe da dama sun yi yunkurin takaita zirga-zirga zuwa cikinsu, yayin da annobar ke kara yawaita a wasu yankuna.
A bangaren larabawa, kasar Saudiyya ta samu a karon farko mutumin da ya kamu da cutar, wanda asalin dan kasar ne da ya taso daga wani yankin Afrika, kamar yadda AlJazeera ta ruwaito.
Kafin shigar cutar Saudiyya, tuni kasar ta dauki matakin dakile shigowarta, inda ta sanyawa wasu kasashe takunkumin shiga kasar.
Legit.ng Hausa ta yi bincike don gano adadin kasashe 14 da Saudiyya ta dakatar daga shiga cikinta zuwa yanzu, kamar yadda Arab News ta ruwaito.
Sabon nau'in COVID19 na Omicron ya bulla Saudiyya, ta dakatar da zirga-zirgan jirage daga kasashen Afirka 14
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ga su kamar haka:
- Malawi
- Zambia
- Madagascar
- Angola
- Seychelles
- Mauritius
- Comoros
- Afrika ta Kudu
- Namibia
- Botswana
- Zimbabwe
- Mozambique
- Lesotho
- Eswatini
A bangare guda, Moussa Mahamat, shugaban hukumar Tarayyar Afirka, ya ce sanya takunkumin hana tafiye-tafiye da ya biyo bayan bullar nau'in Omicron na Korona rashin adalci ne ga nahiyar Afrika.
Mahamat ya bayyana hakan ne yayin wani taron manema labarai a hedkwatar MDD dake birnin New York a ranar Laraba, TheCable ta ruwaito.
Bayan bullar cutar ba Saudiyya ce kadai ta sanya takunkumi ba, kasashe da dama na duniya da suka ci gaba sun sanya dokar hana zirga-zirga ga Afirka ta Kudu da kuma kasashen da ke makwabtaka da ita.
Idan baku manta ba, Legit.ng Hausa ta ruwaito cewa, gwamnatin Kanada ta haramtawa matafiya daga Najeriya da wasu kasashen Afirka tara shiga kasar.
Da duminsa: Yayinda ake gudun Omicron, Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Shugaban kasar Afrika ta Kudu
Da yake bayyana kokensa, Mahamat ya bayyana sanya takunkumin a matsayin cin mutuncin da ba za a iya tabbatar da shi a kimiyance ko a hankalce ba.
NCDC ta bayyana dalili, ta ce cutar kwalara ta fi Korona kashe 'yan Najeriya
A bangaren Najeriya, Cibiyar Kula da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) ta ce cutar kwalara ta kashe rayuka a Najeriya fiye da yadda ake fargabar barkewar cutar Korona, musamman a shekarar 2021.
Babban Daraktan cibiyar, Ifedayo Adetifa, ya ce kasar ta sami fiye da 3,600 da suka mutu sakamakon cutar kwalara a cikin watanni 11 da suka gabata, Premium Times ta ruwaito.
A bangare guda, adadin wadanda suka mutu sakamakon kamuwa da cutar Korona tun daga shekarar 2020 lokacin da ta faro a Najeriya har zuwa yanzu bai wuce 2,977.
Asali: Legit.ng