Da Duminsa: MTN da wasu kamfanoni 2 sun cancanci fara amfani da 5G, inji NCC
- Gwamnatin Najeriya ta amince wa kamfanonin sadarwa guda uku fara amfani da tsarin sadarwar 5G a kasar
- Kamfanonin MTN, Airtel da Mafab ne suka samu nasarar lashe gwanjon da hukumar NCC ta shirya kan tsarin na 5G
- A baya gwamnatin Najeriya ta amince a fara gwada sabis din 5G a Najeriya, inda tace ta tabbatar da bai da wata illa
Najeriya - Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC) ta sanar da wasu kamfanonin sadarwa guda uku da suka cancanta a matsayin wadanda aka amince da su a gwanjon 5G mai gudun 3.5GHz.
An yi gwanjon ne don tura fasahar amfani da tsarin sadarwa na 5G a cikin kasar nan daga Janairun 2022, The Nation ta ruwaito.
Kamfanonin sun hada da MTN Nigeria plc, Mafab Communications Limited da kuma Airtel Networks Limited.
Sanarwar hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Daraktan hulda da jama’a na hukumar ta NCC, Dr Ikechukwu Adinde.
Nigerian Tribune ta ruwaito shi yana cewa:
“Dangane da ka’idojinta na gwanjon keke da keke, Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC) ta sanar da cewa kamfanonin sadarwa guda uku sun cancanta a matsayin wadanda aka amince da su na yin gwanjon tsarin 3.5 gigahertz (Ghz) mai zuwa don dasa tura hanyoyin sadarwa na 5G a kasar."
Gwamnatin Buhari ta amince a fara aiki da fasahar 5G a Nigeria
A baya, Majalisar Zartarwa ta Tarayyar Nigeria, FEC, ta amince a fara aiwatar da tsarin fasahar sadarwar ta 5G.
An amince da fara aiwatar da shirin shimfida fasahar ta 5G din a yayin taron mako-mako na FEC da Shugaba Muhamamdu Buhari ya jagoranta a ranar Laraba.
Femi Adeluyi, hadimin ministan sadarwar da tattalin arzikin zamani, Isa Ali Ibrahim (Pantami) ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a shafin Facebook.
Asali: Legit.ng