Wata sabuwa: Najeriya za ta fara bai wa kasar Chadi wutar lantarki
- Gwamnatin Najeriya ta amince da cewa za ta fara bai wa kasar Chadi da ke da makwabtaka da ita wutar lantarki
- Ministan wutar lantarki, Injiniya Abubakar Aliyu, ya tabbatar da hakan a ziyarar da jakadan Chadi a Najeriya, Abakar Saleh Chahaimin ya kai masa
- A cewar jakaden kasar Chadin, wannan al'amarin zai inganta alaka tare da amfanar kasashen biyu matukar hakan ya tabbata
Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce ta fara shirin bai wa kasar Chadi da ke da makwabtaka da Najeriya wutar lantarki.
Idan za mu tuna, gwamnatin kasar Chadi ta roki a farfado da tattaunawar da aka fara kan cewa Najeriya za ta fara bata wutar lantarki, aminiya Daily Trust ta ruwaito.
Jakaden kasar Cahdi a Najeriya, Abakar Saleh Chahaini ne ya mika wannan kokon barar a yayin ziyarar da ya kai wa ministan wutar lantarki na Najeriya a Abuja, Injiniya Abubakar Aliyu.
Abakar Saleh Chahaimi ya sanar da cewa, a lokutan da suka shude, kasashen biyu sun fara kulla yadda Najeriya za ta dinga bai wa Chadi wutar lantarki amma ba a kai ga kulla yarjejeniyar ba.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Saboda hakan ne ya sake mika kokon bararsa gaban ministan domin ya tabbatar da cewa kasashen biyu za su yi amfani da shirin, aminiya Daily Trust ta ruwaito.
A cewar jakaden, dayar yarjejeniyar da bankin duniya ya dauka dawainiya ta kawo wuta daga kasar Kamaru zuwa Chadi, za a samu karin hadin kai babu shakka.
A bangaren ministan wutar lantarkin Najeriya, Injiniya Abubakar Aliyu, ya bai wa Chahaimin tabbacin cewa za a cigaba da maganar samar da wutar lantarkin.
Ya ce daraktocin ma'aikatar wutar lantarki da ke da masaniya kan inda aka tsaya a batun, za su cigaba da duba lamarin.
Bayan shafe fiye da wata 6 cikin duhu, Zulum ya sanar da ranar da za a dawo da lantarki a Maiduguri
A wani labari na daban, Gwamna Jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum na jihar Borno ya bada tabbacin cewa za a dawo da wutar lantarki a Maiduguri da kewaye cikin kwanaki 30, Daily Trust ta ruwaito.
Babban birnin jihar ta Borno ta kasance cikin duhu tun lokacin da 'yan ta'adda suka lalata layukan lantarkin garin da ke hanyar Maidugri zuwa Damaturu watanni 11 da suka gabata.
Yayin da ya ke gabatar da kasafin kudi ta shekarar 2022 a gaban majalisar jihar, a ranar Talata, gwamnan ya ce ana kokarin dawo da lantarki a garin kamar yadda ya zo a ruwayar ta Daily Trust.
Asali: Legit.ng